An samu raguwar haihuwa a Saudiyya – Masana

Masana sun gano wasu dalilai biyar da suka jawo raguwar haihuwa a tsakankanin mata a kasar Saudiyya, inda suka bayyana rashin yin aure da wuri a matsayalin babban dalili.  daya daga cikin masu binciken ya ce a shekarar 2013 da kuma bara an samu raguwar ne da kusan kashi uku cikin 100. Amma duk da […]

An samu raguwar haihuwa a Saudiyya – Masana
An samu raguwar haihuwa a Saudiyya – Masana

Masana sun gano wasu dalilai biyar da suka jawo raguwar haihuwa a tsakankanin mata a kasar Saudiyya, inda suka bayyana rashin yin aure da wuri a matsayalin babban dalili. 

daya daga cikin masu binciken ya ce a shekarar 2013 da kuma bara an samu raguwar ne da kusan kashi uku cikin 100. Amma duk da raguwar kasar ta ci gaba da zama ta biyu wajen samun haihuwa a yankin Tekun Fasha, inda kasar Oman take ta daya. Har ila yau, Saudiyya ta samu raguwar haihuwa a cikin shekaru 10 da suka wuce. Wannan ya sa masanan ke tunanin cewa kasar ba ta bukatar kara daukar matakan kayyade iyali musamman saboda yadda kasar take fuskantar karancin ma’aikata. Hakan ya sa take dogaro da baki ’yan kasashen waje.
Biciken ya bayyana dalilin da ke sa rashin yin aure akan lokaci tsakanin maza da mata da karatu da aiki da kuma matsalolin tattalin arziki. Hakazalika, an bayyana tsadar rayuwa da kuma yadda ake samun tsawon shekaru masu yawa tsakanin haihuwa zuwa haihuwa, sabanin yadda ake samun shekara daya zuwa biyu a baya. Har ila yau, an danganta raguwar haihuwar da barin ciki tsakankanin matan da shekarunsu suka haura 40.
Wani likitan cututtukan mata da na yara Dokta Hamad al- Sufyan ya bayyana wa jaridar Arab News dalilai biyar da suka jawo raguwar haihuwar wadanda suka hada da teba da rashin cin abinci mai lafiya da ciwon siga da hawan jini da kuma shan taba sigari. A cewarsa wannan ya kawo raguwar jama’ar kasar.