An samu sabbin masu dauke da Coronavirus 4 a Legas
Gwamnatin Jihar Legas ta bayar da sanarwar samun wasu mutane hudu masu dauke da cutar Coronavirus. Kwamishinan lafiya na Jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana haka a wajen wani taron manema labarai. Ko a jiya Laraba ma an bayyana samun mutane biyar dauke da kwayar cutar ta Cornavirus a Najeriya. Kwamishinan lafiyan, ya ce a […]
Gwamnan Legas Sanwo-Olu
Gwamnatin Jihar Legas ta bayar da sanarwar samun wasu mutane hudu masu dauke da cutar Coronavirus.
Kwamishinan lafiya na Jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana haka a wajen wani taron manema labarai.
Ko a jiya Laraba ma an bayyana samun mutane biyar dauke da kwayar cutar ta Cornavirus a Najeriya.
Kwamishinan lafiyan, ya ce a yanzu haka gwamnatin jihar na ci gaba da bankado wasu mutane dubu 1,300 don binciken lafiyar su.
Farfesa Akin, ya ce bayan gwajin da aka yi wa mutum 19 ranar Laraba, cikinsu aka gano karin mutum hudu da suke dauke da cutar coronavirus.
A yanzu haka an kebe dakin masu kula da irin wannan annobar a asibitin Yaba da ke Legas, tun bayan gwajin da aka yi wa wata mata da ta dawo daga Birtaniya aka tabbatar ta kamu da cutar Coronavirus.