An samu sabon mai dauke da Coronavirus a Abuja

Hukumar da ke Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum guda mai dauke da cutar Coronavirus a Abuja. Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter. “An tabbatar da wani sabon kamuwa da COVID-19 a Yankin Babban Birnin Tarayya”, inji sanarwar. […]

An samu sabon mai dauke da Coronavirus a Abuja

Wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya sun kai 30

Hukumar da ke Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum guda mai dauke da cutar Coronavirus a Abuja.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

“An tabbatar da wani sabon kamuwa da COVID-19 a Yankin Babban Birnin Tarayya”, inji sanarwar.

Hakan ya kawo yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a yankin zuwa hudu, yayin da adadin wadanda aka tabbatar a kasa gaba daya ya kai 27, inji hukumar ta NCDC.

Daga cikin 27 din dai an salami mutum biyu bayan sun yi jinya. Har yanzu dai ba a samu wanda ya mutu ba a Najeriya sakamakon kamuwa da cutar.

An samu mutum 10 ɗauke da Coronavirus a Abuja da Legas

Coronavirus: Hukumar jiragen kasa ta lashe amanta

Kafin wannan na babban birnin Najeriyar dai, a jihar Oyo ma dai an tabbatar da samun mai dauke da cutar.

A yanzu dai 19 daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya a jihar Legas suke, hudu a Yankin Babban Birnin Tarayya, biyu a jihar Ogun, yayin da jihohin Ekiti da Oyo ke da guda ko wanne.

Tuni dai hukumomi a Najeriyar suka rufe daukacin filayen jirgin sama na kasar ga jiragen da ke shigowa daga waje.

An kuma shawarci wuraren ibada da su guje wa tara mutane fiye da 50 a lokaci guda; yayin da aka rufe makarantu a jihohi da dama.

 

 

 

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato