An samu sabuwar bullar Cutar COVID-19 a Kuros Riba

An samu sabuwar bullar cutar COVID-19 a Jihar Kuros Riba bayan shafe shekaru uku da rashin samun bullarta a Najeriya.

An samu sabuwar bullar Cutar COVID-19 a Kuros Riba

Rigakafin COVID-19

An samu sabuwar bullar cutar COVID-19 a Jihar Kuros Riba bayan shafe shekaru uku da rashin samun bullarta a Najeriya.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Henry Ayuk, ya tabbatar da bullar cutar a Kalaba yayin da yake ganawa da Aminiya a garin.

Ayuk ya bayyana cewa cutar ta bulla ne ta hannun wani bakon daga kasar Sin wanda ke aiki da kamfanin Lafarge.

Bakon ya iso Najeriya, Kuros Riba, a ranar 17 ga watan Maris 2026, kuma ba da jimawa ba ya kamu da cutar.

Kwamishinan ya ce lamarin ya girgiza shi matuka, inda aka kai mara lafiyar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba (UCTH). Binciken kwararrun likitoci ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar COVID-19.

“An yi gwajin samfurin larurar tasa, likitoci sun tabbatar da cewa cutar COVID-19 ce yake dauke da ita,” inji kwamishinan.

A cewar Dokta Yewande Olatunde, jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Kuros Riba, ana zaton a ranar 19 ga watan nan ne cutar ta fara nuna karfinta a jikin mara lafiyar, lamarin da ya sa aka dauki matakin gaggawa na kai shi asibiti.

Gwamnatin Jihar Kuros Riba ta tabbatar da cewa an killace mara lafiyar a asibiti domin kauce wa yaduwar cutar a jihar, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.