An samu saniyar da ta fi kowace tsawo a Amurka

Wata saniya mai tsawon kafa shida da inci hudu, mallakar wata mata da ke zaune a garin Orangebille da ke jihar Illonois ta Amurka, ta zama doguwar duniya. Mai wannan saniya, Patty Hanson ta cika da murna a lokacin da ta samu sakon i-mail daga Kundin shararrun abubuwan duniya na Guinness Book of Record, inda […]

An samu saniyar da ta fi kowace tsawo a Amurka
An samu saniyar da ta fi kowace tsawo a Amurka

Wata saniya mai tsawon kafa shida da inci hudu, mallakar wata mata da ke zaune a garin Orangebille da ke jihar Illonois ta Amurka, ta zama doguwar duniya. Mai wannan saniya, Patty Hanson ta cika da murna a lokacin da ta samu sakon i-mail daga Kundin shararrun abubuwan duniya na Guinness Book of Record, inda aka karrama saniyarta da wannan matsayi na daraja..

Mai wannan saniya, ta ce ta nemi wannan matsayin ne, a lokacin da likitan dabbobi ya auna tsawon saniyar da nauyinta. Don haka a karshen watan Mayun bana, sai ’yan uwa da abokai suka fara baza hotunan bidiyon wannan saniya mai lakabin Blosom. Kuma jami’a kula da lafiyayyar dabbbobi na Orangebile sun turo likitan dabbobi, ya zo ya auna saniyar.
Hanson ta bayyana cewa wannan matsayin da saniyarta ta samu abin alfahari ne ga gonarta ta Orangebile. Hanson dai ta samu wannan saniya ne to tana ’yar maraka, saboda haka ta ci gaba da kiwonta, hart a kai matsayin da take a yau.