An samu sulhu a masarautar Sakkwato
An cimma sulhu a sabanin da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da daya daga cikin manyan ‘yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba. Zaman ya biyo bayan kwashe kwanaki da wasu manyan sarakunan Arewacin Najeriya suka yi suna kokarin sasanta manyan sarakan biyu. Sulhun ya kai zangon karshe ne […]
An cimma sulhu a sabanin da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da daya daga cikin manyan ‘yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba. |
Zaman ya biyo bayan kwashe kwanaki da wasu manyan sarakunan Arewacin Najeriya suka yi suna kokarin sasanta manyan sarakan biyu.
Sulhun ya kai zangon karshe ne ranar Asabar da ta gabata a wani zaman da aka yi a fadar mai alfarma Sarkin Musulmi da ke birnin Sakkwato.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daya daga cikin manyan sarakuna biyar da suka jagoranci wannan sulhun da Sarkin Gwandu, da Sarkin Kontagora da kuma Etsun Nupe.
“Mun kawo shi wajen mai alfarma sarkin Musulmi ya tuba ya ba shi hakuri; mai alfarma ya karbi wannan ya yafe masa (magajin Gari), wannan magana ta wuce,” in ji sarkin Kano Muhammad Sanusi.
Bayan nan ne Magajin Garin Sakkwato wanda shi ma daya ne daga cikin dangin Usman Danfodiyo da ya ajiye sarautarsa kan sabanin da aka samu da mai alfarma sarkin musulmi ya ce duk abin da ya faru ya wuce sannan kuma ya koma kan sarautarsa “Duk wani abu da ya faru a baya ba zai sake faruwa ba duk wani da ka ji ko ka karanta a kaina ko a kan Mai alfarma Sarkon Musulmi ka shafe shi ya wuce ba sauransa”
Danbaba ya shaidawa manema labarai a makon da ya gabata cewar “Ka dauki abin da ya faru a kanmu a matsayin harka ce ta dangi daya, amma na gode wa Allah da Ya sa aka samu damar shawo kan lamarin cikin salama da mutunci da girmama juna. Sarkin musulmi har yanzu shugabana ne jagorana uban musulmin Najeriya, a koda yaushe zan ci gaba da girmama shi a matsayinsa na jagorana abin koyi da kwarjininsa ke karuwa a ko’ina” a cewar Magajin Gari.
Ya ce zai ci gaba da girmama masarautar Daular Usmaniya, sannan kuma ya gode wa duk wasu rukunin mutane da suka shiga cikin sulhunta lamarin sannan ya tabbatar wa mutanen kasar nan cewa Daular Usmaniya za ta ci gaba da zama tsintsiya madaurikin daya.
A ranar Litinin ne da ta gabata, Magajin garin wanda shi ne mutun na uku ma fi girman sarauta a majalisar sarkin Musulmi ya fice a fusace daga wani zaure da suke ganawa da Sarkin.
Daga bisani kuma ya sanar da yin murabus daga kan sarautarsa wanda yake rike da ita tsawon shekara 20, wanda bayan anyi sulhu ya ce ya koma kan sarautarsa.