‘An samu tsafta a harkar jigilar nama a Kano’
A kwanan baya ne gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ta raba wasu babura masu kafa uku (Keke Napep) guda 100 ga ‘ya’yan kungiyar masu dakon nama a babbar mayanka da ke Jihar Kano. Aminiya ta ziyarci wannan mayanka don ganin yadda za a fara dakon naman da wadanan […]
A kwanan baya ne gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ta raba wasu babura masu kafa uku (Keke Napep) guda 100 ga ‘ya’yan kungiyar masu dakon nama a babbar mayanka da ke Jihar Kano.
Aminiya ta ziyarci wannan mayanka don ganin yadda za a fara dakon naman da wadanan sabbin babura zuwa wurare daban-daban a fadin jihar.
A zantawarta da shugaban kungiyar Abubakar Yakubu Garba, ya bayyana cewa sukan gudanar da aikinsu na jigilar ne daga karfe 6:30 na safe zuwa karfe 12:00 na rana. Hakazalika, sukan kai nama cikin lungu da sakon jihar, inda suke rarraba shi ga masu sayarwa. “mukan zo da sassafe mayanka daga nan sai a zuzzuba mana naman da za mu kai wurin masu sayarwa a cikin baburanmu.
Daga cikinmu akwai wadanda ake kai wa Sabon Gari da ‘Yankanba da Tarauni da Unguwa Uku da Bachirawa da sauran unguwannin kananan hukumomin cikin birnin Kano. “Kasancewar wadanan baburan suna da wurin zuba kaya wadanda suke da murfi a yanzu nama yakan kasance cikin tsafta. Ba kamar ada ba wanda yawanci duk da cewar mukan yi kokarin rufewa, amma ba ya rufuwa duka hakan yakan sa kuda ya rika binsa.
Har ila yau, mu kanmu mun sami tsafta a jikinmu, domin ada ba zai taba yiwuwa mu dauki dakon nama a babur ba tare da ya bata mana jiki ba. Hakan ya sa a da ba ma yin wanann aiki da tufafi masu kyau, amma a yanzu hakan ya zama tarihi,” inji shi.
Shugaban ya ce duk da cewa ba kyauta gwamnatin ta raba musu wadannan babura ba, amma sun yi murna da samunsa “kasancewar ba ya ga daukar naman da muke yi mukan yi amfani da baburan wajen dakon sauran kayayyakin yau da kullum, inda sukan kara samun abin kai wa bakin salati gwamnati ta ba mu kowane babur a kan cewa za mu rika biyan naira 600 a kullum, idan kuma muka kai watanni 18 baburan za su zama namu.”
Har ila yau, wani daga cikin masu aiki da babur mai suna, Auwalu Ibrahim wanda ya bayyana cewa ya dauki tsawon shekaru 20 yana sana’ar dakon naman, ya bayyana cewa duk da cewar sun sami wadannan babura sai dai aikin ba ya samuwa “kasancewar masu sayar da naman ba su ciniki yanzu, hakan ya sa mu ma ya shafi aikinmu. Za ki tarar mai siyen kafa biyu zuwa uku yanzu bai fi kafa daya yake saye ba,” inji shi.