An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba
Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara huɗu a gidan yari.

Wata kotu a Birnin Paris na Ƙasar Faransa, ta samu tsohon shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Faransa, Bernard Squarcini, da laifin zamba da amfani da dukiyar jama’a ba bisa ƙa’ida ba.
Squarcini, mai shekaru 69, ya jagoranci hukumar tsaron cikin gida ta Faransa daga 2008 zuwa 2012.
Bayan ya bar aiki, kamfanin LVMH ya ɗauke shi aiki a matsayin mai bayar da shawara kan harkokin tsaro.
A ranar Juma’a da ta gabata, kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari, inda biyu daga ciki aka dakatar da su.
An same shi da laifin amfani da abokan tsaronsa don cimma burinsa, har da samun bayanan sirri na kamfanin LVMH.
Za a ba Squarcini damar yin zaman gidansa, amma sanye da munduwa ta lantarki.
Haka kuma, an ci shi tarar Yuro 200,000 tare da dakatar da shi daga duk wani aiki da ya shafi leƙen asiri ko bayar da shawara na tsawon shekaru biyar.
Lauyoyinsa sun ce za su ɗaukaka kara kan hukuncin.