An samu wani mutum da rai bayan shekara 17 a karkashin kasa
Masu iya magana sun ce duk mai rabon ganin badi ko ana ruwan kibiya sai ya gani. Wata tawagar masu hakar ma’adanai daga yankin dinjiang da ke kasar China sun ga abin mamaki yayin da suke hakar ma’adainai lokacin da suke kwashe kasa sai wani sashe ya bude inda suka ga wawakeken kogo na tsohuwar […]
Masu iya magana sun ce duk mai rabon ganin badi ko ana ruwan kibiya sai ya gani. Wata tawagar masu hakar ma’adanai daga yankin dinjiang da ke kasar China sun ga abin mamaki yayin da suke hakar ma’adainai lokacin da suke kwashe kasa sai wani sashe ya bude inda suka ga wawakeken kogo na tsohuwar wata mahakar madanai da girgizar kasar da ka yi shekaru 17 da suka gabata ta yi wa illa, wanda hakan ya sa a ka yi watsi da ita saboda wurin ya rufta. Suna cikin kwashe kasar wurin sai kawai suka ga wani mutum a ciki mai suna Cheung Wai, dan kimanin shekaru 59 a duniya.
Cheung Wai yana daya daga cikin masu hakar ma’adanan da girgizar kasar ta rutsa da su a lokacin da suke yin aiki tun shekarar 1997. Shi kadai Allah ya yi yana da sauran shan ruwa a duniya. Nan take aka dauke shi aka kai shi asibiti inda ake ci gaba da duba lafiyarsa sai dai ya fita daga hayyacinsa kwarai da gaske amma likitoci sun bayyana fatan zai murmure.
Mujallar kasar da ke buga labaran hakar ma’adinai ta ruwaito cewa Shi dan Wai ya kasance a karkashin kasa tare da gawarwakin ’yan’uwansa su 78 wadanda girgizar kasar ta rutsa da su yayin da suke hakar ma’adanai. Ya rayu ne ta hanyar shakar iska mai kyau ta hanyar daya daga cikin hanyoyin iskar da girgizar kasar ba ta yi wa illa ba wacce ta hada cikin ramin da wajensa.
Ya rika cin beraye da tana da kuma tsutsotsi da ke rayuwa a karkashi kasar wacce yayin shinkafar da aka jibge a wurin da ruwan da ke karkashin kasar wurin ya taimaka masa kwarai da gaske, wanda hakan ya taimaka Wai ya sami dan walawa. Duk da haka ya binne dukkan abokanensa daya bayan daya a karkashin kasar ba tare da taimakon kowa ba inda ya shafe kimanin shekara guda yana binne su.
Hadari a wurin hakar ma’adinai ba sabon abu ba ne a kasar Sin duk da matakin da gwamnati take dauka na rage aukuwar hadarin inda mutum dubu hudu ke mutuwa duk shekara. Lamarin Cheung ya ja hankalin duniya inda ya zarta dan kasar Birtaniya mai suna Geoff Smith da ya shafe kwanaki 142 a karkashin kasa, wanda ya sa aka binne shi don ya dauki kambin wanda ya fi kowa dadewa a karkashin kasa.