An samu wata bishiyar zogale mai dauke da sunan Allah a Edo
Aminiya ta tattauna da Yarima Momoh Abdullahi, dan shekara 63 a duniya, mazaunin garin Auchi da ke Jihar Edo, wanda ke zaune a titin Akhelaye Street. Shi ne ya shuka itatuwan zogale a gidansa, wadanda kuma aka samu rubutun sunan Allah a jikinsu. A tattaunawar, ya bayyana yadda aka yi ya samo irin zogalen da […]
Aminiya ta tattauna da Yarima Momoh Abdullahi, dan shekara 63 a duniya, mazaunin garin Auchi da ke Jihar Edo, wanda ke zaune a titin Akhelaye Street. Shi ne ya shuka itatuwan zogale a gidansa, wadanda kuma aka samu rubutun sunan Allah a jikinsu. A tattaunawar, ya bayyana yadda aka yi ya samo irin zogalen da kuma lokacin da ya fara ganin sunan Allah a jikinsu:
Ko za ka yi mana bayani a kan wadannan itatuwan zogale da sunan Allah ya bayyana a jikinsu?
To, lallai kafin in fara yin bayanin da ka neme ni da shi, zan fara da yi wa Allah da Ya kaddarta ba ni wannan kyauta godiya saboda ba ko wa yake samun hakan ba, ni ma kaina wannan abin ban taba zato ko tunanin zan same shi, ko zai faru a wurina ba.
Wadannan bishiyoyin na zogale, shuka su ka yi ko sun tsirane kurum kamar yadda sauran itatuwa suke tsira a daji?
A’a, ba haka ba ne. Ni na shuka su da hannuna kamar yadda kake ganinsu tushe guda hudu, daga cikinsu akwai mai shekara uku akwai kuma mai shekara biyu da rabi.
To, ta yaya ka yi ka gane cewa wadannan itatuwan suna dauke da sunan Ubangiji a jikinsu?
Yadda na gane alamar sunan Ubangiji a jikin wadannan itatuwan shi ne, bayan na dawo daga tafiyar da na yi zuwa ganin wata bishiya da na samu labarin sunan Allah ya bayyana a jikinta, na dawo ba da dadewa ba sai na fara ganin wasu alamun rubutu a jikin wadannan bishiyoyin zogalen amma da yake ni ban yi karatu ba sai na je na kira limamin unguwarmu Malam Ahmadu, na gaya masa abin da na gani. Sai ya bi ni muka zo ya gani, sai ya gaya mani cewa wannan sunan Ubangiji ne.
Ko za ka gaya mana yadda ka yi har ka samu tushen wadannan itacen zogalen?
Yadda na yi na samu irin har na dasa shi ne, da na je Ibadan ina dawowa sai na ga irin zogalen, wanda ake tsirarwa a sayar; sai na yi sha’awa na saya na zo na dasa, suka girma, suka zamo bishiyoyi guda uku. Wannan da kake gani na hudun, mai rubutun sunan Allah a jiki, bai wuce shekara biyu ba da na dasa shi.
Ka ce zuwanka Ibadan ne ka zo da irin wannan zogalen, shin a nan cikin garinku Auchi babu zogalen ne ya sa ka sayo irin daga can?
Ba haka lamarin yake ba, muna da zogale da dama a nan garin Auchi da kewayensa amma ra’ayi ne da kuma ga yadda Allah Ubangiji ya kadarta zai faru ta wannan hanyar, na sayo wannan tushen itacen daga Ibadan din, na kawo gidana na da sa su.
Ko za ka iya bayyana mana lokacin da ka fara ganin wannan rubutu na sunan Allah a wadannan bishiyoyin?
A lokacin da na fara ganin wannan alamar, shi ne a ranar 11 ga Agustan bana amma daga faruwar wannan abin al’ajabin, malaman addini da sauran mutane da dama suka rika yin tururuwa suna zuwa nan gidana domin shaida wa idanunsu. A cikin malaman akwai babban limamin garin Auchi kuma da dama a cikin mutanen da suka zo ina ba su ganyayen itacen idan suka neme ni da yin hakan ba tare da na karbi kwabonsu ba kuma ban san tunaninsu da karbar ganyayen ba. Sai dai suna ci gaba da gode mani idan na tsinki ganyen na ba su. A cikinsu akwai Musulmi kuma akwai Kirista.
Ka taba yin tunani za ka samu irin wannan baiwar a rayuwarka?
Lallai hakika ni ban taba yin tunani zan samu irin hakan ba amma da ikon Allah ga shi na samu. Don haka ina kara godiya ga Allah.
Ya batun iyali kuma, kana da su?
Babu shakka ina da iyali, a yanzu haka ina da matar aure daya kuma ina da ’ya’ya biyar, mata hudu da namiji daya; su ne Khadija, Muslim, Rahmatu, Marya da Zainab. Wasu daga cikinsu akwai masu aikin gwamnati.
Ko kana da wani sako da kake bukatar a isar maka ga ’yan uwa Musulmi da sauran al’ummar Najeriya?
To, lallai sakon da nake son ku isar mani ga ’yan uwa shi ne, kowane Musulmi ya ji tsoron Allah kuma su bar gaba da juna, su hada kai a kan abin da zai tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai ma’ana.