An samu yaro mai hakora 232 a Indiya
Wani yaro dan shekara 17 a kasar Indiya ya yi fama da ciwon kumburin baki, al’amarin da ta kai ga likitocin sun cire masa hakora 232. Yaron ya fito daga garin Buldhana, don haka ya ziyarci asibitin Sir J.J. a makonni biyun da suka wuce, ganin kumburin bakinsa sai aka shiga yi masa gwaje-gwaje, inda […]
Wani yaro dan shekara 17 a kasar Indiya ya yi fama da ciwon kumburin baki, al’amarin da ta kai ga likitocin sun cire masa hakora 232. Yaron ya fito daga garin Buldhana, don haka ya ziyarci asibitin Sir J.J. a makonni biyun da suka wuce, ganin kumburin bakinsa sai aka shiga yi masa gwaje-gwaje, inda likitoci suka gano yana dauke da kananan hakora har 232.
“Da farko ba a gano hakikanin abin da ke dmaunsa ba, amma sai muka yanke shawara shiga aikin fida,” a cewar Sunanda Dhibare-Palwankar, shugaban sashen aikin hakora a asibitin.
Yayin da gungun likitoci suka shiga, sai suka cika da mamakin ganin wasu kananan hakor masu tsawon sentimita bakwai.
“Da suka fara kirga adadinsu, sai suka gano har guda 232, kowane ya yi tsiro, ya fito yana cin gashin kansa, inda suke ta girma za su zama manyan hakora. Irin wannan ciwo na hakori yana da wuyar aiki, a cewar likitocin, domin yana haifar wa mutum matsalar kasa cin abinci ko hadiya, har ta kai ga kumburinsu ya mamaye fuska baki dayanta.
Ashik Gabai, yaro dan aji tara a makarantar Buldhana da ke garin bidarbha a yankin Gabashin Maharashtra, ya fara ganin kumburin ne, a shekarun da suka gabata. Jin cewa babu zafi, sai ya kyale bai kula ba.
Tuni dai aka yi masa aiki a karkashin tsarin kulawa da daukar nauyin gwamnati, musamman ma saboda ya fito daga cikin iyalai matalauta kasar Indiya.