An samu zakaru a gasar tenis ta Legas
kwararrun ’yan wasan kwallon Tenis maza da mata da ke rukuni daban-daban sun fara fafatawa a makon jiya don lashe gasar da kamfanin Sterling Asset Management and Trustees Limited ya shirya inda aka samu zakaru a wasanni daban-daban. Gasar wacce aka kammala a ranar Juma’ar d ta gabata ta fara ne da bangaren maza zalla […]
kwararrun ’yan wasan kwallon Tenis maza da mata da ke rukuni daban-daban sun fara fafatawa a makon jiya don lashe gasar da kamfanin Sterling Asset Management and Trustees Limited ya shirya inda aka samu zakaru a wasanni daban-daban.
Gasar wacce aka kammala a ranar Juma’ar d ta gabata ta fara ne da bangaren maza zalla a rukunin farko da na biyu a bangaren kwallon tenis na otel din Ikoyi da ke yankin Ikoyi a Jihar Legas.
Wadanda suka ganewa idonsu sun bayyana cewa an yi fafatawa mai zafi a tsakanin ’yan wasan bisa tsari da nuna dattaku ga alkalan wasan.
Sauran bangarorin da suka fafata sun hada da na mata zalla da kuma rukunin kwararru na maza zalla da ake yi wa lakabi da Mens’ double da rukunin kwararru da ake yi wa lakabi da beteran single da super beteran singles.
Shugaban sashen kwallon tenis na otel din Ikoyi 1938, Adetayo Osuntogun ya ce an sanya kyaututtuka masu kayatarwa a dukkan rukunonin gasar.
Ya ce gasar ta kara armashi ne saboda kwararrun da suke fafatawa a gasar.
A rukunin maza zalla na daya da aka fatata a ranar Litinin ta makon jiya, Dele Kuti ya samu nasara ne a kan abokin karawarsa Dare Olude da ci 3 da babu.
A wasan kusa da na karshe da aka gudanar a tsakanin dan wasa Seye Oki da Hon Ko Lee, ya yi armashi domin Seye ne ya lallasa Hon Ko Lee da ci 3 da nema.
Shi ma Oluwole Soetan ya lallasa Osuntogun da ci 3 da nema al’amarin da ya sa Soetan zai kara da Dapo Akindiji wanda ya lallasa Yinka Adeyemi.
Segun Adegoke shi ya zama zakara a rukunin maza zalla na 2 bayan da ya ci dukkanin wasanninsa guda biyar.
Tuni su ma rukunin mata suka fara fafatawa a ranar Laraba inda aka samu zakaru a rukunoni da dama.