An samu zaki yana yawo a kan titi a kasar Kuwait

Wani dan karamin zaki ya kubuto daga wani gida, inda ya yi ta yawo a kan wani titi da ke gefen kasuwa, kamar yadda jaridar Gulfnews ta ruwaito. Wannan zaki da ya bayyana a kan wani titin birnin Bayan ta kasar Kuwait. Wani mai mota ya lallabe zakin ya shigar da shi cikin motarsa, sannan […]

An samu zaki yana yawo a kan titi a kasar Kuwait

Dan zakin a bayan motaWani dan karamin zaki ya kubuto daga wani gida, inda ya yi ta yawo a kan wani titi da ke gefen kasuwa, kamar yadda jaridar Gulfnews ta ruwaito. Wannan zaki da ya bayyana a kan wani titin birnin Bayan ta kasar Kuwait. Wani mai mota ya lallabe zakin ya shigar da shi cikin motarsa, sannan ya kira ’yan sanda su taimaka masa.
Wannan dan karamin zaki ya cika bayan motar. “Mai motar ya zauna a cikin mota tare da zaki, sai kuma zakin ya fara nuna hadari. Don haka ya kira ’yan sanda,” a cewar majiyar ’yan sanda.
Tuni hukumomi suka dauke zaki zuwa wani wuri a gundumar Bayan da ke kudu da babban birnin. A halin yanzu ’yan sanda na neman mai zakin, wanda a ke tunani ya ajiye shi ba bisa ka’ida ba. Domin a kasar Kuwait ana ganin ajiyar irin wadannan dabbobi wata alfarma ce ta masu hannu da shuni.
Shugaban Jami’an ’yan wsanda masu aikin ceto, Zuhair Al Nasr Allah, ya gargadi mutane su yi takatsantsan wajen ajiye irin wadannan dabbobin.
“Bai kamata a ce irin wadannan dabbobin sun zama hadari ga iyalai ko makwaftansu ko gama-garin mutane,” inji shi.
Ana ta kai farmaki a kasuwanni da ke kasashen Bahrain da Kuwait don tabbatar da cewa ba a hada-hadar dabbobin daji.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan