An samu zinare a cikin Ba’indiye
Likitoci a kasar Indiya sun samu curi 12 na zinare a cikin wani dan kasuwa bayan da suka yi masa aiki a wani asibiti da ke birnin Delhi.Mutumin ya kai kansa asibiti ne saboda neman lafiya daga yawan hararwa da yake fama da ita wanda yace ta samo asali ne daga hadiyar wani murfin gorarruwa […]
Likitoci a kasar Indiya sun samu curi 12 na zinare a cikin wani dan kasuwa bayan da suka yi masa aiki a wani asibiti da ke birnin Delhi.
Mutumin ya kai kansa asibiti ne saboda neman lafiya daga yawan hararwa da yake fama da ita wanda yace ta samo asali ne daga hadiyar wani murfin gorarruwa da yayi bisa kuskure a lokacin da suke wata takaddama da mai dakinsa. Bayan da likitocin suka dauki hoton cikin ne sai suka gudanar da aiki don cire masa murfin gorar amma sai suka samu curin 12 na zinare wanda ya kai nauyin giram 400 Yuro dubu 13 da 900, wanda ya yi daidai da Naira miliyan uku.
Bayan ya murmure ne, sai ‘yansanda suka gudanar da bincike a kan sa inda suka gano cewa tun da fari ba murfin gora ya hadiya ba, kuma suka tabbatar da cewa dan kasuwar da ke sana’ar sayar da zinare, ya hadiyi zinaren da gangan saboda boyesu daga idon jami’an hukumar Kwastam din Indiya a lokacin da yake kokarin shigo da shi kasar. Hukumomi dai sun karbe zinare nan take, saboda laifin yin fasakwaurinsu da dan kasuwar ya aikata.
Wani babban likitan fida a asibitin yace bai taba ganin irin wannan al’amarin ba, a tsowon tarihin aikinsa, ya kara da cewa aikin cire zinaren ya kwashe su tsowon sa’a uku kafin su kammala.