An sanar da Vinicius cewa zai lashe kyautar Ballon d’Or

Vinicius ya taka rawar gani sosai a gasar Zakarun Turai da La Liga da Madrid ta lashe a kakar bara.

An sanar da Vinicius cewa zai lashe kyautar Ballon d’Or

Vinicius Junior

A ranar 28 ga watan Oktoba ne za a gudanar da bikin bayar da kyautar Ballon d’Or a filin wasa na Threatre du Chalet da ke birnin Paris.

Duk da cewa saura wata guda a gudanar da bikin, da alama dai tuni aka bayyana wanda ya lashe kyautar.

A cewar jaridar wasanni ta ‘Marca’, xan wasan Real Madrid da Brazil Vinicius Junior na shirin karɓar mashahuriyar kyautar ta zama gwarzon ɗan wasa a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa, tuni Hukumar Kwallon Kafa ta France Football da ita ce hukumar bayar da kyautar, ta sanar da dan wasan na Real Madrid cewa zai lashe kyautar Ballon d’Or.

Dan wasan na Brazil ya taka rawar gani sosai a gasar Zakarun Turai da La Liga da Real Madrid ta lashe a kakar bara kuma yana daya daga cikin waɗanda suka lashe kyautar sannan ya zama guda cikin waɗanda za su maye gurbin su Cristiano Ronaldo tare da abokin wasansa Jude Bellingham da na Manchester City Rodri.

A kakar wasa ta 2023/2024, kididdigar ƙwarewar da Vinicius ya yi da suka fi burgewa sun haɗa da kwallaye bakwai jimilla da ya zura a wasannin Zakarun Turai da wasu 19 a gasar La Liga – 11 daga cikinsu ya zura su a ragar manyan kungiyoyi 10 a gasar.

A takaice, idan har dan wasan Real Madrid ɗin ya lashe kyautar Ballon d’Or ba zai zama abin mamaki ba.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano