An sanya dokar hana fita a biranen jihar Gombe

Gwamnatin jihar Gombe ta sanya dokar hana fita a birane jihar bayan wani rikici ya kaure tsakanin matasan Kirista da wasu matasa a babban birnin jihar a safiyar yau Asabar. Mukaddashin Sakataren Gwamnatin jihar Mista James Pisagih, ya sanar wanda Gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwambo ya sanya hannu inda dokar ta fara aiki nan ta […]

An sanya dokar hana fita a biranen jihar Gombe

Gwamnatin jihar Gombe ta sanya dokar hana fita a birane jihar bayan wani rikici ya kaure tsakanin matasan Kirista da wasu matasa a babban birnin jihar a safiyar yau Asabar.

Mukaddashin Sakataren Gwamnatin jihar Mista James Pisagih, ya sanar wanda Gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwambo ya sanya hannu inda dokar ta fara aiki nan ta ke, saboda kaucewa barkewar rikici a wasu yankunan jihar.

Dokar hana fitar za ta fara aiki ne daga karfe 3 na rana zuwa karfe 6 na safiyar gobe Lahadi, za a sassauta dokar idan komai ya lafa, jami’an tsaron zasu ci gaba da binciken lamarin.