Dokar hana fita a Ekiti sai baba ta gani

Gwamnan Jihar Ekiti ya sanya dokar hana fita ta sa’a 24 har sai abin da Allah Ya yi a fadin jihar. An sanya dokar ce bayan ‘yan daba da wasu bata-gari sun kwace zanga-zangar #EndSARS a jihar, tare da tayar da hankulan jama’a. Gwamnan ya ba da umarnin tsawaita dokar hana fitar ne a daidai […]

Dokar hana fita a Ekiti sai baba ta gani

Shugaban Zauren Majalisar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti

Gwamnan Jihar Ekiti ya sanya dokar hana fita ta sa’a 24 har sai abin da Allah Ya yi a fadin jihar.

An sanya dokar ce bayan ‘yan daba da wasu bata-gari sun kwace zanga-zangar #EndSARS a jihar, tare da tayar da hankulan jama’a.

Gwamnan ya ba da umarnin tsawaita dokar hana fitar ne a daidai lokacin da wadda ya sanya da farko ke dab da karewa.

Hakan na dauke ne a cikin sakon Sakataren Watsa Labaran gwamnan, Yinka Oyebode ya fitar.

Karin labarin na tafe…