An sanya dokar hana fita a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta daga safe zuwa dare na tsawon sa’a 24 a cikin garin Kaduna da kewaye sakamakon rikicin da ya haddasa rasuwa da raunata wasu jama’a da dama a yankunan. Majiyarmu ta bankado cewa, tun lokacin da aka sace sarkin Adara, Agom Adara, Mista Maiwada Galadima, aka fara […]
Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta daga safe zuwa dare na tsawon sa’a 24 a cikin garin Kaduna da kewaye sakamakon rikicin da ya haddasa rasuwa da raunata wasu jama’a da dama a yankunan.
Majiyarmu ta bankado cewa, tun lokacin da aka sace sarkin Adara, Agom Adara, Mista Maiwada Galadima, aka fara samun rahotanni tashin hankali wanda ya fara daga Kasuwar Magani inda aka kashe akalla mutum 55 a cikin kwana uku da suka gaba ta.