An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba
An gano cewa lamura sun lafawa a unguwannin da abin ya shafa kwanaki biyu da suka gabata bayan tura jami’an tsaro, sai dai kuma ’yan sa-kan sun sake ƙaddamar da wasu hare-haren a ranakun Alhamis da Juma’a.
An sanya dokar hana fita a ƙaramar hukumar Karim-Lamido biyo bayan ƙaruwar tashe-tashen hankula da kashe mutane da lalata dukiya da wasu da ake zargi ’yan sa-kai ne masu ɗauke da makamai suke yi.
Rahoranni sun bayyana cewa, ana zargin wasu rukunin ’yan sa-kan da kai hare-hare da dama a kan al’ummomin Wurkum da ke kewayen Didango da Mutum Daya, Kodai, Gurum, da sauran unguwanni, waɗanda suka yi sanadin asarar rayukan mutane da dama.
- Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano
- Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki
An gano cewa lamura sun lafawa a unguwannin da abin ya shafa kwanaki biyu da suka gabata bayan tura jami’an tsaro, sai dai kuma ’yan sa-kan sun sake ƙaddamar da wasu hare-haren a ranakun Alhamis da Juma’a.
An kuma gano cewa, tsanantar hare-haren ta tilasta wa Shugabar ƙaramar hukumar, Madam ɓirginia Bambur sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a yankin, ciki har da garin Karim wanda shi ne babban birnin ƙaramar hukumar Karim-Lamido.
Shugabar Majalisar ƙaramar hukumar ta Karim-Lamido, Virginia Baba Bambur, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, shawarar sanya dokar hana fita “A Karim da Didango da ɗaukacin yankunan da abin ya shafa ta zama dole saboda tsanantar rikicin, ci gaba da kai hare-hare da kuma asarar rayuka da dukiya sakamakon tashin hankalin da ya dabaibaye waɗannan yankuna,” in ji ta.
Ta kuma umarci ɗaukacin jami’an tsaro, wato Sojoji da ’Yan sanda da jami’an tsaron farin kaya DSS, da na Civil Defense NSCDC da sauransu da ke ƙaramar hukumar da su lura da wannan umarni kuma su tabbatar an kiyaye dokar.
Virginia Baba Bambur ta ci gaba da cewa, gwamnati za ta gudanar da bincike na tsaf domin gano ainihin tushen lamarin, sannan ta tabbatar da cewa an hukunta waɗanda ke da hannu a ciki.