An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa

An tsinci gawar amaryar ne kwance cikin jini a gidanta da ke Hadejia.

An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare da kafa wuraren bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Zainab Ibrahim.

An yanke wannan shawara ne a taron da aka gudanar a Hadejia, wanda ya haɗa jami’an majalisar masarautar da hukumomin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma.

Manufar taron ita ce samo mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin.

Da yake jawabi a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a.

Ya buƙaci shugabannin yankin da su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

An tsinci gawar Zainab Ibrahim, wacce aka ɗaura mata aure a baya-bayan nan, kwance cikin jini a gidanta da ke unguwar Warware.

Lamarin ya tayar da hankalin al’umma, lamarin da ya tilasta hukumomi ɗaukar matakan tsaro cikin gaggawa.

Bayan tattaunawa, an amince da sanya dokar hana fita daga ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na Asuba, tare da kafa wuraren binciken tsaro.

Shugaban kwamitin tsaro na Ƙaramar Hukumar Hadejia, Ahmed Ari, ya bayyana cewa dokar hana fitar za ta taimaka wajen rage aikata laifuka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya kuma roƙi al’ummar yankin su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da nasarar waɗannan matakai.