An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a Kano

Dokar ta fara aiki daga karfe 6 na yammacin yau Laraba.

An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 biyo bayan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an baza jami’an tsaron hadin gwiwa a fadin birnin Kano domin tabbatar da dokar hana fita.

“Bisa tanadin da kundin tsarin mulki ya bai wa rundunar ’yan sandan Najeriya tare da jami’an tsaro na cikin gida da hukumomin tabbatar da doka da oda a jihar, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tsara dabaru kan wannan al’amari tare da yin kira ga jama’ar jihar don guje wa tayar da yamutsi.

“Ana kira ga mazauna Jihar Kano da su lura cewa tuni aka aike da jami’an tsaron hadin gwiwa zuwa lungu da sako domin tabbatar da bin dokar hana fita ta sa’o’i 24, wanda zai fara aiki daga karfe 6 na yammacin ranar Laraba, 20 ga watan Satumba zuwa 6 na yammacin Alhamis, 21 ga watan Satumba, 2023.

“Duk wanda aka kama ya karya doka kuma zai fuskanci fushin doka.

“Daga karshe, ina mika godiyata ga daukacin al’ummar jihar nan masu son zaman lafiya tare da rokon su da su kasance masu bin doka da oda,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa an shiga fargaba a jihar bayan hukuncin da kotu ta yanke na ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Da yammacin ranar Laraba ne mutane da dama suka shiga rufe shagunansu da wuraren kasuwancinsu saboda fargabar hare-haren bata-gari.

Jihar ta sha fama da rikici, barna da kone-kone a cikin watan Maris bayan da aka ayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan na Maris.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna