An sanya dokar ta-baci a wasu jihohin Amurka saboda tsananin sanyi
Amurka tana fuskantar matsanancin sanyi wanda aka shafe shekaru masu yawa ba a samun irinsa ba. Ban da tsananin sanyi da take fama da shi a yanzu, akwai kuma wata iska mai karfi daga yankin Arctic na Arewacin duniya da ka iya kawo matsanancin sanyi na kasa da ma’aunin Celsius -53. Jami’ai a Jihar Iowa […]
Amurka tana fuskantar matsanancin sanyi wanda aka shafe shekaru masu yawa ba a samun irinsa ba.
Ban da tsananin sanyi da take fama da shi a yanzu, akwai kuma wata iska mai karfi daga yankin Arctic na Arewacin duniya da ka iya kawo matsanancin sanyi na kasa da ma’aunin Celsius -53.
Jami’ai a Jihar Iowa na gargadin mutane su guji shakar numfashi mai yawa, kuma su rage yin magana idan sun fita wajen gidajensu.
Akalla mutum miliyan 55 ne ake sa ran yanayin matsanancin sanyi zai shafe su.
An ayyana dokar ta-baci a jihohin tsakiyar Amurka kamar Wisconsin da Michigan da Illinois, har ma da jihohin da ke Kudancin kasar kamar Alabama da Mississippi.
John Gagan, wani jami’in hukumar kula yanayi ta Amurka ya ce irin wannan tsananin sanyin na zuwa ne sau daya a tsawon shekaru, kamar yadda BBC ya ruwaito yana fada.
Ana kuma hasashen sanyin zai ci gaba da karuwa. Sannan kuma jami’ai sun ce sanyi a birnin Chicago zai iya zarce na yankin Antarctica.
An dai soke fiye da sauka da tashin jiragen sama 1,100 daga ciki da wajen Amurka tun ranar Talata.
Lamarin ya kai har hukumomi a yankin tsakiyar Amurka na rufe dubban makarantu da shaguna da ofisoshin gwamnati.
Sannan hukumomin sun samar wa mutanen da ba su da wurin zuwa wuraren da za su fake daga wannan matsanancin sanyin a biranen Amurka da dama har da Jihar Milwaukee.