An sanya ma’aikatan fadar shugaban kasa cikin shiri saboda dawowarsa

An kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata inda aka sanya ma’aikatan fadar shugaban kasa cikin shirin ko-ta-kwana saboda dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kasar Ingila. Jaridar Aminiya ta gano cewa tuni wadansu daga cikin iyalan shugaban kasar da jami’an da ke kare lafiyar matarsa suka dawo Abuja tun jiya. Daya daga cikin masu taimaka […]

An sanya ma’aikatan fadar shugaban kasa cikin shiri saboda dawowarsa


An kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata inda aka sanya ma’aikatan fadar shugaban kasa cikin shirin ko-ta-kwana saboda dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kasar Ingila.
Jaridar Aminiya ta gano cewa tuni wadansu daga cikin iyalan shugaban kasar da jami’an da ke kare lafiyar matarsa suka dawo Abuja tun jiya.
Daya daga cikin masu taimaka wa matar shugaba kasar ya bayyana cewa Hajiya Aisha Buhari ta yiwu ta dawo Najeriya gobe Laraba.