An sanya masu karbar burodi a keji don daidaita sahu

Hotunan wadansu mutanen Siriya da suke cikin halin ni ’yasu da aka wallafa a Damascus babban birnin kasar, sun nuna yadda aka tilasta wadansu mutane shiga kejin karfe inda suka yi layi don karbar burodi wanda hakan ya janyo muhawara a shafukan Intanet. Hotunan da aka yi ta yadawa a kafafen sada zumunta na zamani, […]

An sanya masu karbar burodi a keji don daidaita sahu

Hotunan wadansu mutanen Siriya da suke cikin halin ni ’yasu da aka wallafa a Damascus babban birnin kasar, sun nuna yadda aka tilasta wadansu mutane shiga kejin karfe inda suka yi layi don karbar burodi wanda hakan ya janyo muhawara a shafukan Intanet.

Hotunan da aka yi ta yadawa a kafafen sada zumunta na zamani, sun nuna yadda aka jera mutane a cikin kejin ne don tabbatar da an bi ka’idojin bin sahu wajen karbar burodin.

A cewar rahotanni, an ware maza daban da mata da kuma sojoji a cikin kejin.

Masu bibiyar shafukan sada zumunta na amfani da hotunan da aka wallafa wajen nuna yadda tattalin arzikin kasar ya tagayyara da kuma yadda jama’ar garin ke rayuwa.

Kasar Siriya ta shafe shekara tara tana yaki, wanda hakan ya yi sanadiyyar raba miliyoyin jama’a da gidajensu.

A farkon wannan wata ne Gwamnatin Siriya ta kirkiro da hanyar takaita amfani da burodi ga kowane dan kasar a gidajen burodin kasar wanda yin hakan ya sa wadansu zama cikin yunwa.

A cikin tsarin da gwamnatin kasar ta fitar magidanci mai iyali biyu zai samu burodi daya ne kawai kowace rana inda magidanci mai iyali bakwai ko sama da haka zai samu burodi hudu ne kawai shi da iyalinsa.

Wadansu na amfani da hotunan wajen sukar gwamnatin Siriya da Shugaba Bashar al-Assad yayin da wasu hukumomin kasar kuwa cewa suka yi ya kamata gwamnati a Damascus ta rubutu wata alama a kasa da masu karbar burodi za su bi sahu maimakon sanya su a cikin keji.

A cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya, kashi 90 cikin 100 na ’yan kasar Siriya na rayuwa cikin talauci, sakamakon rikicin tattalin arzikin a Lebanon ga kuma bullar cutar Coronavirus da kuma takunkumin Amurka.

A kullum abubuwan amfanin yau da kullum kamar, man fetur da fulawa da shinkafa da sukari suna kara tsada, wanda hakan ya sa wadansu ba su iya sayensu.

Rahoto ya bayyana cewa, an kiyasta sama da mutum miliyan 11 na mutanen Siriya na bukatar agajin gaggawa don su rayu.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7