An sanya ranar zaɓen ƙananan hukumomi a Jigawa 

Hukumar ta tabbatar da dalilin da ya sanya ta ɗage zaɓen a baya.

An sanya ranar zaɓen ƙananan hukumomi a Jigawa 

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Jigawa (JISIEC), ta sanya ranar 5 ga watan Oktoba domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.

Shugaban hukumar, Alhaji Awwal Muhammad ne, ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki, a Dutse a ranar Juma’a.

Muhammad, ya tabbatar da shirin hukumar na gudanar da sahihin zaɓe a kananan hukumomi 27 na jihar.

Ya sanar da cewa a baya hukumar ta sanar da ɗage zaɓen kansiloli, daga watan Yuni, 2024 zuwa Yuni, 2025, bayan gyaran dokar zaɓen jihar.

“Duk da haka, kuna sane da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke na baya-bayan nan da ta umarci dukkanin gwamnatocin jihohi da su kafa ƙananan hukumomin da aka zaɓa ta hanyar dimokuradiyya a jihohinsu, nan take.

“A bisa bin hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na baya-bayan nan, JISIEC, a matsayinta na hukuma, ta ga ya zama dole ta yi biyayya ga hukuncin, sannan ta buƙaci baki ɗaya da a sake gyara dokar zaɓen jihar.

“Saboda haka an sanya ranar Asabar 5 ga watan Oktoba, 2024 a matsayin sabuwar ranar da za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Jigawa,” in ji shi.

Ya buƙaci hukumomin tsaro, shugabannin gargajiya da na addini, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin, ƙungiyoyin mata, shugabannin matasa, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin al’umma da su mara wa hukumar baya, domin cimma burin da ake so.

Muhammad, wanda ya jaddada ƙudirin hukumar na gudanar da sahihin zaɓe, ya yaba wa masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bai wa hukumar, a kokarinta na gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci a jihar.