… An sanya siyasa a batun dokar ta-baci – Halifa Hassan Yusuf
Galadiman Damaturu kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PRP a Jamhuriya ta Biyu, Halifa Hassan Yusuf ya ce an sanya siyasa, a cikin batun dokar ta-bacin da ake sa wa jihohi uku na yankin Arewa maso Gabas. A tattaunawarsa da Aminiya a Damaturu, Galadiman ya ce, abin da ya sa suke zargin an sayna siyasa a batun […]
Galadiman Damaturu kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PRP a Jamhuriya ta Biyu, Halifa Hassan Yusuf ya ce an sanya siyasa, a cikin batun dokar ta-bacin da ake sa wa jihohi uku na yankin Arewa maso Gabas.
A tattaunawarsa da Aminiya a Damaturu, Galadiman ya ce, abin da ya sa suke zargin an sayna siyasa a batun dokar ta-bacin shi ne jihohin uku duk Jam’iyyar adawa ta APC ke mulki ga shi kuma zabubbuka sun karato, don so ake yi wadannan jihohi sun koma hannun Jam’iyyar PDP ko ta halin kaka tunda in babu tsaro a hannun gwamnonin ba su da katabus sai yadda aka yi da jihohinsu.
Alhaji Hassan Yusuf ya ce babu wata fa’ida da sake kafa dokar za ta samar tunda a baya ba ta haifar da komai ba, sai dada tabarbarar da al’amura, “In aka dubi abubuwan da suka rika faruwa a lokacin dokar ta-baci na baya-bayan nan kamar kashe daliban makarantun Gujba da Buni Yadi da na Mamudo da na Damaturu da na baya-bayan nan na garin Potsikmu da kuma kwace kananan hukumomin Gujba da Gulani a Jihar Yobe da kwace wasu a jihohin Borno da Adamawa dole mu ce akwai boyayyiyar manufa a cikin wannan lamarin,” inji shi.
Don haka ya ce ba daidai ba ne a sake mayar da wannan doka kasancewar an sa an sa an kuma sake sawa har sau uku, amma ba ta yi amfani ba. “Idan an ce saboda tashin bama-bamai ne yawaitar fashewar bama bamai ne, jihohi irin su Kano da Kogi da Neja da Bauchi da Kaduna da kuma Abuja ana samun irin haka, za mu iya cewa kusan duk Najeriya ba ta da lafiya, amma da ya ke akwai siyasa ciki sai jihohin uku aka sa wa dokar,” inji Hassan Yusuf.
Ya bukaci ’yan majalisa da kada su amince da kara wa’adin dokar tunda ba ta da wani alfanu.