An sanya wa jaririya sunan abin wasa

An sanya wa jaririya sunan wani shahararren abin wasa da ake yawo da shi ana latse-latse (mobile game), mai lakabin Wang Zherongyaoda ke ma’anar Martabar sarkauna; sunan jaririyar dai an yi masa rajista a di’an da ke Arewa maso Yammacin kasar Sin a Lardin Shaandi, kamar yadda jaridar kasuwanci ta Sin (Chinese Business biew) ta […]

An sanya wa jaririya sunan abin wasa

An sanya wa jaririya sunan wani shahararren abin wasa da ake yawo da shi ana latse-latse (mobile game), mai lakabin Wang Zherongyaoda ke ma’anar Martabar sarkauna; sunan jaririyar dai an yi masa rajista a di’an da ke Arewa maso Yammacin kasar Sin a Lardin Shaandi, kamar yadda jaridar kasuwanci ta Sin (Chinese Business biew) ta ruwaito.

Mahaifin jaririyar ya fito ne daga Lardin Hebei, kuma mahaifiyarta daga Lardin shaandi. Bayan da aka haifi jaririyar ranar 1 ga Agustar bana, saio suka yanke cewa su yi rajistar sunanta a birnin di’an.

Mahaifin wannan yarin na aiki ne a kamfanin fasahar sadarwa, kuma sunan ya bijiro masa ne daga wannan abin wasa, a cewar mahaifiyar jaririyar.

Jami’an ’yan sandan yanklin sun ce sunan bai saba tsarin dokar rajistar suna ba, wadda ta gindaya sharadin cewa dole ne suna ya kasance ya kama daga haruffa biyu zuwa hudu na harshen mutanen Sin.

Ra’ayin masu takaddama a kan sunan a shafukan intanet ya bambanta, inda wasu ke ganin abin da iyayen jaririyar suka aikata abin sha’awa ne, yayin da wasu ke kallon illar da ke tattare da sunan a kan yarinyar in ta girma.

Kayan wasan dai wani mashahurin kamfanin intanet ne na Tencent ya kera shi, inda ya samu gagarumar nasara tare da haifar da rudani, musamman ga hukumomin da ke kadin al’amura irin wadannan a kasar Sin.

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi

Ɗan shekara 85 ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe