An sasanta batun zargin Zango ya boye wata ’yar fim
Masu iya magana sukan ce duk abin da ya yi farko zai yi karshe, a yanzu dai an sasanta takaddamar da ta kaure tsakanin jarumi Adam A. Zango da masu rikon jaruma Rahama Yaseer.Idan ba za a manta ba dai wata mata da ake kira Mama Uwani ta shiga gidan rediyo a Kano inda ta […]

Masu iya magana sukan ce duk abin da ya yi farko zai yi karshe, a yanzu dai an sasanta takaddamar da ta kaure tsakanin jarumi Adam A. Zango da masu rikon jaruma Rahama Yaseer.
Idan ba za a manta ba dai wata mata da ake kira Mama Uwani ta shiga gidan rediyo a Kano inda ta zargi jarumin da boye Rahama tsawon kwana 40, hakan ne ya sanya Hukumar Yaki da Fataucin Jama’a da kuma Sauran Laifuffuka ta kasa (NAPTIP), reshen Jihar Kano ta shiga al’amarin.
Daga baya ne Hukumar ta gayyaci masu ruwa da tsaki daga dukkan bangarorin ofishinta don gano gaskiyar al’amarin.
Majiyar tamu daga ofishin Hukumar (NAPTIP) ta ce hukumar ta sasanta batun takaddamar da ake yi a kan yarinyar (Rahama). Ta kuma karyata batun cewa ta yarje wa Adam Zango ya ci gaba da rikon Rahama, duk da cewar yarinyar ta ce tafi son zama a hannunsa kasancewar ta yi sabo da ‘ya’yansa da sauran mutanen gidansa.
“A ranar Juma’ar da ta gabata ne Hukumar ta zauna da masu rikon yarinyar a kan batun, mun kuma yanke hukuncin za ta koma makaranta ba za ta sake fitowa a fim ba. Hukumar ta gargadi dan uwan yarinyar mai suna Yasir, wanda ya rika kai ta wurin masu fim, inda hukumar ta ce kada ya sake sanya ta a fim. An riga ma an yi magana da mahaifiyarta wacce a yanzu haka take zaune Saudiyya, wacce ta ce za ta zo ta dauki ‘yarta. Sai dai kafin ta zo a yanzu za ta ci gaba da zama a hannun marikiyarta wacce ta yi alkawarin ci gaba da kula da ita da karatunta daidai gwargwadon karfinta” Inji majiyarmu.
Wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun jarumin, Abu Sarki, inda ya ce sun koma ofishin hukumar a Juma’ar (ta makon jiya) da ta gabata, inda kafin lokacin hukumar ta nemi su ci gaba da rike yarinyar, kuma bangaren da ke rikon yarinya sun amince da hakan, “hakan ya sanya muka ce a ba mu sati daya don mu yi tunani a kai, bayan mun koma ne muka amince za mu ci gaba da rikonta, amma daga baya sai mai rikon yarinyar ta koma wurin hukumar, sannan ta ce za ta ci gaba da rikonta don ta cika ladanta. Muka ce babu damuwa, da ma Zango zai taimake ta ne, kuma duk da haka ba zai fasa yi mata alherin da ya saba ba.” Inji Abu Sarki.