An sassare tsohon minista da adda a Afirka ta Tsakiya

Wani tsohon minista Musulmi a kasar Afirka ta Tsakiya, mai suna Joseph Kalite ya rasa ransa lokacin da wasu mutane suka sassare shi da adduna a babban birnin kasar, Bangui.Hakan ya faru a daidai lokacin da fada ya sake kaurewa kwana daya da kama aikin sabuwar Shugabar kasa Misis Catherine Samba-Panza.Baya ga haka an kashe […]

An sassare tsohon minista da adda a Afirka ta Tsakiya

Joseph KaliteWani tsohon minista Musulmi a kasar Afirka ta Tsakiya, mai suna Joseph Kalite ya rasa ransa lokacin da wasu mutane suka sassare shi da adduna a babban birnin kasar, Bangui.Hakan ya faru a daidai lokacin da fada ya sake kaurewa kwana daya da kama aikin sabuwar Shugabar kasa Misis Catherine Samba-Panza.
Baya ga haka an kashe akalla mutum tara, lokacin da wani ayarin jama’a da galibinsu Kiristoci ne suka kai hari suna kwasar ganima a Unguwar Miskine da galibin mazaunanta Musulmi ne a ranar Juma’ar da ta gabata.
Tsohon Minista Joseph Kalite, wanda ya rike Ma’aikatar Gidaje yana fitowa daga cikin wata tasi ne aka auka masa kamar yadd wani dan uwansa ya shaida wa kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ta tarho.
’Yan kungiyar Anti-Balaka sun auka masa da adduna da itatuwa har suka kashe shi,” inji dan uwan wanda ya nemi a sakaya sunansa. Ya ce wani surukinnsa da ke tare da Kalite a lokacin harin ya samu ya gudu.
Daga baya an karbo gawarsa aka kai masallacin Ali Babolo inda Rueters ya ruwaito ya ga gawar da aka sassara. “Ba ya rike da kowane irin mukami a Seleka, an ma kore shi daga Seleka, amma tunda shi Musulmi ne sai suka yi masa kisan rashin imani,” Mamoud Hissene Mataimakin Shugaban kungiyar Matasa Musulmi ya shaida wa Rueters.
’Ya’yan kungiyar Anti-Balaka ta Kiristoci suna amfani da haramtawa da kwace makaman ’ya’yan kungiyar Selelka ta Musulmi wajen kai hare-hare a kan Musulmi marasa rinjaye da suke zargi da hada kai da Seleka.
Mayakan Anti-Balaka sun fara dibar ganima a shagunan unguwar Miskine a ranar Juma’ar da ta gabata, wanda hakan ya jawo mayar damartani daga mayakan Selelka, inda aka rika jin karar harbe-harben manyan bindigogi a daidai lokacin da jama’a suka rika gudu don tsira da rayukansu.
A makon jiya ne aka zabi Magajiyar birnin Bangui Misis Samba-Panza a matsayin Shugabar kasar ta riko bayan da manyan kasashen duniya suka matsa wa Shugaba Michel Djotodia, jagoran hadakar Seleka wanda ya sauka a ranar 10 ga Janairu.
Ana sa ran Samba-Panza ta kafa sabuwar gwamnati a ’yan kwanaki masu zuwa.