An sassauta dokar hana fita a Azare

Gwamnatin Bauchi ta sassauta dokar hana fita a garin Azare zuwa awa 12

An sassauta dokar hana fita a Azare

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sassauta dokar hana fita na awanni 24 da aka sanya a Karamar Hukumar Katagum.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Barista Ibrahim Muhammad Kashim, ta ce “Da ga yanzu dokar za ta soma aiki ne daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Sannan ta bukaci mazauna yankin da su cigaba da biyayya ga matakan da gwamnatin take ɗauka wajen dawo da doka da oda a yankin.

Kashim ya ce, “Majalisar tsaron jihar Bauchi ta yi nazarin dokar da aka sa kuma ta yi la’akari da yadda ake samun dawowar zaman lafiya a cikin garin Azare da kewaye na Karamar Hukumar Katagum.

Don haka ta, “ta amince da sassauta dokar hana fita da aka kakaba wa yankin,”

Tun da farko an sanya dokar hana fita ne, bayan tashe-tashen hankula da aka samu a yankin yayin zanga-zangar da aka gudanar na neman kawo karshen yunwa wanda ta rikiɗe zuwa tarzoma da lalata kayan gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane a garin Azare.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS