An sassauta dokar hana fita a biranen Gombe
Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da sassauta dokar hana fita da aka sanya a biranen jihar Gombe zuwa awa 12, wanda zai fara aiki daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kullum. A jiya Lahadi ne aka fara sassauta dokar hana fitar daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe. […]
Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da sassauta dokar hana fita da aka sanya a biranen jihar Gombe zuwa awa 12, wanda zai fara aiki daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kullum.
A jiya Lahadi ne aka fara sassauta dokar hana fitar daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe.
Akwai rahotanni da ke bayyana cewa, a daren jiya Lahadi ana zaman fargaba a wasu yankunan jihar. Kamar yadda mukaddashiin Sakataren Gwamnatin jihar Mista James Pisagih a madadin Gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwambo ya sanar.