Mutfwang ya sassauta dokar hana fita a Jos

Dokar hana zirga-zirga a garin Jos ta koma karfe 2 na rana zuwa 6 na yamma

Mutfwang ya sassauta dokar hana fita a Jos

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang

Gwamnatin Jihar Filato ta sassauta dokar takait fita da ta sa a garin Jos sakamakon tarzoma sa sace-sace a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Gwamna Caleb Mutfwang ya sassauta dokar ta awa 24, inda yanzu za ta fara aiki daga karfe 2 na rana zuwa 6 na yamma.

Daraktan yada labaran gwamnan, Gyang Bere, ya sanar da cewa an samu sassaucin ne sakamakon ingantuwar al’amura a yankin Jos-Bukuru.

“Daga Laraba, 1 ga Agusta 2024, dokar hana zirga-zirga ta koma daga karfe 2 na rana zuwa 6 na yamma

“Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang, na jinjina ga jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen aiwatar da dokar hana fita ta awa 24 da aka sanya da farko.

“Kazalika ya jaddada muhincin ci gaba da lura da yanayin tsaron al’umma domin dakile motsin bata-gari.

“Jama’ar yankin Jos-Bukuru kuma ana kira a gare su da su ba wa jami’an tsaro hadin kai wajen kai rahoton ayyukan bata-gari domin a duki mataki a kan lokaci..

“Al’ummar jihar Filato gaba dayanku Gwamna Mutfwang na yaba muku bisa kisin kasa a kuka nuna wajen bin umarnin dokar da aka sanya da kuma ba wa jami’an tsaro hadin kai domin cigaban jiharmu”.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS