An sassauta dokar hana fita a kananan hukumomi 3 a Yobe

Jama’a na da damar gudanar da harkokinsu daga karfe 12:00 na rana zuwa 5:00 na yamma.

An sassauta dokar hana fita a kananan hukumomi 3 a Yobe

Gwamnan Yobe Mai Mala Buni

Gwamnatin Yobe ta sanar da sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya a wasu ƙananan hukumomi uku na jihar.

Gwamnatin ta ce a yanzu jama’a na da damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum daga karfe 12:00 na rana zuwa 5:00 na yamma.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Alhamis din da ta gabata gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Potiskum, Nguru, da kuma Gashua sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da ta rikide zuwa tarzoma.

Sai dai wata sanarwa da mashawarcin gwamnan jihar na musamman kan harkokin tsaron, Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya ya fitar a yau Lahadi, ya ce an sassauta dokar bayan da aka samu ci gaba a harkar tsaro a garuruwan Potiskum, Gashua da Nguru.

Sanarwar ta umarci hukumomin tsaro da su kula da yanayin da ake ciki a yanzu don tabbatar da cewa bata-gari ba su yi amfani da wannan dama ba wajen kawo abin da zai haifar da rashin bin doka da oda.

Gwamnan na rokon al’umma su cigaba da addu’ar neman zaman lafiya mai daurewa a dukkan Jihar da ma kasa baki daya.

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas