An sauke shugabannin kungiyar masu shayi ta Jihar Filato

An sauke shugabannin kungiyar masu shayi ta Jihar Filato, bayan cikar wa’adinsu na shekaru 4 kan shugabancin kungiyar. An sauke shugabannin ne a wajen taron da ’yan kungiyar suka gudanar a garin Jos, babban birnin Jihar Filato. Har’ila yau a wajen taron an nada shugabannin riko na kungiyar mutum 5, karkashin jagorancin shugaban kungiyar na […]

An sauke shugabannin kungiyar masu shayi ta Jihar Filato

An sauke shugabannin kungiyar masu shayi ta Jihar Filato, bayan cikar wa’adinsu na shekaru 4 kan shugabancin kungiyar. An sauke shugabannin ne a wajen taron da ’yan kungiyar suka gudanar a garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

Har’ila yau a wajen taron an nada shugabannin riko na kungiyar mutum 5, karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Alhaji Shu’aibu Abubakar.

Da yake jawabi a wajen taron shugaban kungiyar na kasa kuma shugaban rikon da aka zaba Alhaji Shu’aibu Abubakar, ya bayyana cewa an rushe tsofaffin shugabannin ne bayan cikar wa’adinsu na shekaru 4.

Ya yi kira ga ’ya’yan kuungiyar su basu goyan baya da  hadin kai, domin su gudanar da wannan aiki da aka basu na rikon kungiya a cikin nasara. 

Ya ce zamu sami lokaci ayi tsaftatcen zabe a wannan kungiya, a baiwa duk wanda aka zaba, batare da wata matsala ba. Ya ce kofa a bude take ga duk wanda yake son shugabancin wannan kungiya, ya fito ya tsaya takara. 

“Muna kira ga masu shayi su hada kansu domin su sami nasara a wannan sana’a. Kamfanonin da suke yin kayayyakin shayi da masu gidajen biredi basa son ku hada kai. Sun fi son su ganku a watse ta yadda zasu debo biredin da ya lalace su kawo maku, ta haka  suke ta dora maku bashi. Da yawan masu shayi sun zama bayi, a wajen masu gidajen biredi da masu sayar da kayayyakin shayi, saboda rashin hadin kan ku.”  

Har’ila yau ya yi kira ga masu sana’ar shayi su sani cewa a matsayinsu na masu ciyar da al’umma, ya kamata su rika mutum ta mutane. Kuma su guji yin ha’inci, su tsayar kan gaskiya a wannan  sana’a,  idan suka yi haka zasu sami cigaba. 

Shi ma a nasa jawabin tsohon shugaban kungiyar da aka sauke Malam Ahmed Abubakar ya mika godiyarsa kan wannan dama da aka basu na shugabancin kungiyar tsawon shekara 4 da suka gabata.

Ya ce a shekara 4 da suka yi suna shugabancin kungiyar, sun sami nasarori da dama musamman wajen hada kan ’ya’yan kungiyar. 

Ya yi kira ga ’yan kungiyar  su bai wa shugaban rikon da aka nada goyan baya da hadin kai, har ya zuwa lokacin da za a zabi sababbin shugabannin kungiyar.