An ƙara sassauta dokar hana fita a Jos

Yanzu za a daina fita daga karfe 12 na rana zuwa 6 na yamma

An ƙara sassauta dokar hana fita a Jos

An sauya lokacin aikin dokar taƙaita zirgaa garin Jos na jihar Filato.

Gwamnatin jihar ta sanar cewa daga yanzu an mayar da lokacin hana zirga-zirgar jama’a ƙarfe 12 na rana zuwa 6 na yamma.

Sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Gyang Bere, ya ce sabon sassaucin zai fara aiki ne ranar Alhamis din nan.

Karo na biyu ke nan da ake sauya lokacin dokar a cikin ƙasa da awa 24.

Hakan na nufin karin awa biyu a kan sassaucin da aka samu da farko, wadda aka hana zirga-zirga daga karfe 2 na rana zuwa 6 na yamma.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS