An sauya wa gawar Fir’auna kabari a Masar

An sassaka akwatin kowace gawa yana kamanceceniya da wanda ke kwance a cikinsa.

An sauya wa gawar Fir’auna kabari a Masar

Gawar Fir’auna

Rahotanni daga Kasar Masar sun bayyana cewa, an sauya wa gawar Fir’auna makwanci tare da sauran tsoffin sarakunan kasar zuwa Kudancin al Kahira, babban birnin kasar.

Mahukunta gidan tarihin kasar sun ce wannan aiki na sauya kaburburan tsoffin sarakunan ya dauke su makonni biyu bayan kwashe su da aka yi a wani kasaitaccen biki.

Aminiya ta ruwaito cewa, makonni biyu da suka gabata ne aka fitar da Fir’auna, Sarkin Masar da ya yi zamani tare da Annabi Musa (A.S) da kuma sarakunan kasar na shekaru aru-aru da suka shude a tarihi.

Yayin bikin da aka gudanar, an dauke tsoffin Sarakuna 22 – maza 18 da mata huda, zuwa sabon gidan tarihin, inda aka sanya hoton kowane sarki a kusa da akwatin gawar da suke ciki da kuma taimakawa wajen fahimtar tarihinsu gabanin mutuwarsu fiye da shekara 3,000 baya.

An sassaka akwatin kowace gawa yana kamanceceniya da wanda ke kwance a cikinsa.

Gawar Fir’auna yayin sauya mata akwati

An kuma ware wa kowane Fir’auna mota ta musamman da za ta dauki akwatin gawarsa da ke lullube da sinadarin Nitrogen don tabbatar da cewa ba su samu wata illa ko barazana ba.

Masu binciken kimiyyar tarihi sun gano tsoffin sarakunan ne a wata tsohuwar makabartar sarakuna da tarihinta ya kai shekara 1871, a Deri Al Bahari da ke Luxour.

Mafi dadewa a cikinsu shi ne Seqenenre Tao, sarki na karshe a Daula ta 17, wanda ya rayu a karni na 16 kafin zamanin Annabi Isa (AS), kuma tarihi ya nuna ya yi mummunan karshe.

ِِAkwai kuma Ramses II, wanda wasu masana tarihi ke ganin shi ne ya yi zamani da Annabi Musa (AS); sai kuma Seti I, da Ahmose-Nefertari.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC