An rage wa ma’aikatan Kano lokutan aiki albarkacin watan Ramadana
An buƙaci ma’aikata su ribaci matakin domin bauta wa mahaliccinsu da yi wa jihar da kasa addu’a.
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta rage wa ma’aikatanta lokutan gudanar da aiki a watan Ramadan mai kamawa.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da a hannun Sakataren Ofishin Shugaban Ma’aikata na jihar, Umar Muhammad Jalo.
- A gaggauta ceto ɗaliban da aka sace a Kaduna — Tinubu
- An gurfanar da mutum 41 kan haƙar ma’adanai a Oyo
Cikin sanarwar dai, a ranakun Litinin zuwa Alhamis ma’aikatan za su fara aiki ne daga karfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na yamma, yayin da za a ci gaba da aiki yadda aka saba a ranakun Juma’a.
Sanarwar ta kuma ce matakin ya biyo bayan yunkurin gwamnatin na bai wa ma’aikatan damar bautawa mahaliccinsu, da kuma yi wa Jihar Kano da ma kasa baki ɗaya addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba.