An saya wa karya mai kafafu shida keken guragu ta Naira dubu  175

Wata mata suna Lauren Salmon da ta mallaki wata karya a garin Orpington da ke birnin Landan na kasar Birtaniya, ta ce wata bakuwa da ta ziyarce ta kuma ta fahimci karyar gidanta mai suna Roo tana da wata baiwa matuka don haka ta saya wa karyar keken guragu ta Fam 400 (daidai da Naira […]

An saya wa karya mai kafafu shida keken guragu ta Naira dubu  175

Wata mata suna Lauren Salmon da ta mallaki wata karya a garin Orpington da ke birnin Landan na kasar Birtaniya, ta ce wata bakuwa da ta ziyarce ta kuma ta fahimci karyar gidanta mai suna Roo tana da wata baiwa matuka don haka ta saya wa karyar keken guragu ta Fam 400 (daidai da Naira dubu 174, da 598).

Bakuwar ta saya wa karyar keken guragun ne don taimaka wa karyar ta ci gaba da gudanar da rayuwarta kamar sauran dabbobin da ba su da nakasa saboda haihuwarta da aka yi da kafafu shida.

Wanda ta mallaki karyar ta yaba da karamcin da bakuwar ta nuna wa karyar. Karyar dai tana da kimanin mako 10 da haihuwa.

Babban abin al’ajabin karyar an haife ta ce da kafafu shida  maimakon hudu, duk da haihuwarta hakan ta kasance tana rayuwa kamar sauran karnuka.

Wannan karyar an rada mata suna Roo ne lokacin da wata dabbar dawa Kangaroo ta goya karyar bayan ta ganta tana tsalle da karin kafafu biyu.

Karyar tana cikin koshin lafiya kamar sauran dabbobi.

Lauren, mai shekara 33, ta sayi Roo ne a wajen kiwon dabbobin na Esseda a karshen watan Yuli, bayan da danta mai suna Luke, ya ga an wallafa tallar karnuka a shafin Intanet.

Wannan karyar tana kyakykyawar alaka da Luke mai shekara 15, wanda yake fama da cutar fata kuma kasancewarsa da karyar ya kara masa kwarin gwiwar gudanar da harkokinsa.

Lauren, ta ce, “Karyar ta taimaka wa dana, na yi murnar kasancewa tare da Roo.”

A cewar Lauren, bakuwar da ta saya wa karyar keken guragun ta yi haka ne don tunawa da karanta da ya mutu don haka ta yanke shawarar yin wani abu da zai kyautata wa karyar.

Bakuwar mai ’ya’ya hudu, ta ce tana da dabi’ar kyautata wa karnuka ne don rashin karenta, “Ina bukatar in ga karyar a cikin wannan keke,” inji ta.

Lauren, ta ce a yanzu haka karyarta ta samu keken da za ta taimaka mata wajen tafiya duk inda take son zuwa, sannan da zarar karyar ta girma za ta rika fita da ita a kekenzuwa wurin shakatawa.