An sayar da ƙoƙon kan dan shekara 14 da ƙafafunsa Naira dubu 70 a Oyo

Ya sayar da ƙoƙon kan da ƙafafun yaron a kan Naira dubu 70.

An sayar da ƙoƙon kan dan shekara 14 da ƙafafunsa Naira dubu 70 a Oyo

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama wani mutum mai suna Muhammad Adekunle da ake zargin ya jagoranci fille kan wani yaro dan shekara 14 mai suna Malik Kareem domin yin tsafin samun kudi da sassan jikinsa.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ayodele Sonubi ne ya bayyana hakan yayin da yake nuna mutumin a wajen taro da ’yan jarida a ofishinsa da ke Eleyele a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo.

Sonubi ya ce bayan samun labarin danyen aikin da ake zargin Adekunle ya jagoranta, sai rundunar ta tura jami’anta wadanda suka kama shi tare da gano ƙoƙon kai da ƙafafun marigayi Malik wadanda ya sayar a kan Naira dubu 70 ga wata mata mai suna Rashidat Akanji da ke kasuwanci a Kasuwar Oje a Ibadan.

Kwamishinan ’Yan sandan ya ce a binciken da suka yi a cikin gidajen wadanda aka kama an gano wasu sassan jikin dan Adam a gidan Adekunle wadanda ya cewa suna daga cikin sassan jikin yaron da suka yaudara suka kashe ne domin yin tsafin samun kudi cikin dare daya da sassan jikinsa.

Kwamishinan ya ce a cikin watan Afrilu da ya gabata Adekunle ya jagoranci irin wannan danyen aiki inda suka kashe wani mai suna Adekola Sodiƙ suka yi watandar sassan jikinsa suka sayar ga masu tsafin samun kudi a Ibadan.

Ya ce tuni jami’ansa suka fara bin sawun sauran mutum biyu da suka tsere bayan kama jagoran nasu.

Ya ce matar da aka kama kan zargin sayen sassan jikin dan Adam domin yin tsafin kudi tana tsare a hannun ’yan sanda zuwa lokacin da za su kammala bincike a gurfanar da su gaban kotu.

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu