An sayar da balama Naira miliyan 13 a Kuwait
An sayar da wata balamar tunkiyar ’yar shekara biyu Dinari dubu 80, wato daidai da Naira miliyan 13 da dubu 280, a kasar Kuwait, kamar yadda jaridar Al Rai ta ruwaito.A rahoton jaridar an yi wa balamar lakabin “Yar Jamus,” a cewar mai tunkiyar, tana da wasu siffofina musamman wadanda ba za a wsamu a […]
An sayar da wata balamar tunkiyar ’yar shekara biyu Dinari dubu 80, wato daidai da Naira miliyan 13 da dubu 280, a kasar Kuwait, kamar yadda jaridar Al Rai ta ruwaito.
A rahoton jaridar an yi wa balamar lakabin “Yar Jamus,” a cewar mai tunkiyar, tana da wasu siffofina musamman wadanda ba za a wsamu a sauran dabbobi ba.
Wanda ya mallaki wannnan tunkiya, Thamer Ubaid Al Dhufairi, ya ce mutum biyu suka biya dimbin kudi don su mallaki balama ‘yar Jamus.’
“An dai fara yin tayi da yi wa tunkiyar farashi, tun da yamma har zuwa wayewar gari,” inji shi.
“Dam un yi tunanin za a kara farashin har sai ta kai Dinari dubu 100, amma sai muka yanke cewa mu rage farashi, don girmama mutane biyun a suka fara taya ’yar Jamus,” a cewarsa, ind aya kara da cewa: “a da sunan wannan balama Istareeh wato hutun wucin gadi, amma daga bisani aka sauya mata suna, bayan da kasar Jamus ta lashe gasar cin kofin kwallon duniya.”