An sayar da littafi mafi tsada a duniya kan Naira biliyan 296 da rabi

An buga littafi mafi tsada a kasar Amurka, inda aka yi gwanjonsa a kan kudi Dala miliyan 14 da rabi, wato daidai da Naira biliyan biyu da miliyan 296; wannan luittafi ya zamo mafi tsada a daukacin littattafan duniya.Litattafin fassarar zabbbura ce, wadda a Turance aka yi wa lakabi da “The Bay Psalm Book” kuma […]

An sayar da littafi mafi tsada a duniya kan Naira biliyan 296 da rabi
An sayar da littafi mafi tsada a duniya kan Naira biliyan 296 da rabi

An buga littafi mafi tsada a kasar Amurka, inda aka yi gwanjonsa a kan kudi Dala miliyan 14 da rabi, wato daidai da Naira biliyan biyu da miliyan 296; wannan luittafi ya zamo mafi tsada a daukacin littattafan duniya.
Litattafin fassarar zabbbura ce, wadda a Turance aka yi wa lakabi da “The Bay Psalm Book” kuma kamfanin dabi’in da ya wallafa shi, shi ne Puritanical settlers, kuma asalin littafin an buga shi ne a shekara ta 1640, sannan an yi gwanjonsa a karkashin jagorancin Sotheby. An fara taya littafin a kan Dala miliyan shida, inda a karshe aka daidaita a kan farashin Dala miliyan 14 da dubu 145, a cewar mai magana da yawun Kamfanin Sotheby.Tuni kamfanin gwanjon kadarorin ya kimanta darajar littafin a kan Dala miliyan 15 zuwa 30, amma har yanzu ba a bayyana wanda ya sayi littafin ba.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan