An sayar da wani kare Naira miliyan 350
A kasar Sin (China) an sayar da wani nau’in kare da ake samu a yankin Tibetan, kusan Dala miliyan biyu (kimanin Naira miliyan 350), lamarin da ya sa ya zama mafi tsadar kare da aka taba sayarwa.Wani mai harkar gidaje, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya biya Yuan miliyan biyu (wato Dala miliyan daya […]
A kasar Sin (China) an sayar da wani nau’in kare da ake samu a yankin Tibetan, kusan Dala miliyan biyu (kimanin Naira miliyan 350), lamarin da ya sa ya zama mafi tsadar kare da aka taba sayarwa.
Wani mai harkar gidaje, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya biya Yuan miliyan biyu (wato Dala miliyan daya da dubu 900) a kan karen dan shekara daya, mai gashi launin ruwan zinari, a wani bikin baje-kolin dabbobi da aka yi a gabashin gundumar Zhejiang, kamar yadda jaridar kianjiang Ebening News ta ruwaito.
“Irin wadannan karnuka suna da jinin zakoki kuma suna da wani babban matsayi a tsakanin jinsinsu”, inji Zhang Gengyun, a yayin da yake yi wa jaridar bayani. Sannan ya kara da cewa an sayar da wani irin wannan karen mai jan gashi a kan Yuan miliyan shida, wato rabin farashin na farko.
Girman karnukan da kuma laya-layan gashinsu, yakan ba su kamannin zakoki, kuma farin jininsu a tsakanin attajiran kasar ta Sin ya haifar da tashin gwauron zabin farashinsu.
Shi dai wannan kare yana da tsawon sentimita 80 (inci 31 ko yadi biyu da inci bakwai) kuma yana da nauyin kilogiram 90 (kusan laba 200), inji Zhang, wanda kuma ya yi nunin yakan yi alhinin sayar da karnukan, wadanda ba wanda aka fadi sunansa a cikin rahoton jaridar.
“Tsintsar karnukan Tibetan na asali, suna da wuyar samu, kamar yadda panda take a kasar nan”, inji shi. Panda wata irin dabba ce a yankunan gashin duniya da kan iya tsayuwa kan kafafunsu biyu kuma suna da tsananin son farautar kifi, abin da ya fi soyuwa cikin abincinsu.
A shekarar 2011 an sayar da wani karen mai jan gashi a kan Yuan miliyan goma, wato Dala miliyan daya da dubu 500 (kimanin Naira miliyan 247), wanda a lokacin shi ne mafi tsadar karen da aka taba sayarwa.