An shafe wata 14 babu cutar Foliyo a Jihar Kaduna
Babban Sakataren Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kaduna (PHCA), Dokta Sufiyan Mu’awiyya Baballe ya ce yanzu wata 14 ke nan ba su samu rahoton bullar cutar shan inna a fadin jihar ba.Dokta Sufyanu Baballe ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din makon jiya a wurin taron taron nazarin yadda ake gudanar da […]
Babban Sakataren Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kaduna (PHCA), Dokta Sufiyan Mu’awiyya Baballe ya ce yanzu wata 14 ke nan ba su samu rahoton bullar cutar shan inna a fadin jihar ba.
Dokta Sufyanu Baballe ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din makon jiya a wurin taron taron nazarin yadda ake gudanar da rigakafin cutar shan-inna a jihar da kuma nemo hanyoyin da za a bi don kawar da cutar baki daya da Hukumar PHCA ta jihar da Hukumar UNICEF suka shirya.
Babban Sakataren ya danganta wannan nasara kan kokarin masu ruwa da tsaki a da suka hada da likitoci da Hukumar UNICEF da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO da sarakuna da malaman addini da ’yan jarida da kungiyoyi da dama da kuma iyayen yara da suke yarda a yi wa ’ya’yansu rigakafin cutar.
A jawabin Kwamishinan Lafiya na Jihar Kaduna, Dokta Joseph Dogo Thot, ya ce gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa ta ga cutar shan inna ba ta sake bullowa a jihar ba.
Ya ce wata 14 da aka yi babu cutar jihar abin alfahari ne kuma abu ne mai faranta rai ga gwamnati da al’ummar jihar baki daya.
Sai ya yi kira ga al’ummar Jihar musamman iyaye maza a kan su ba da hadin kai sosai don rigakafin shan inna a jihar ya ci gaba da samun nasara. Ya ce ba ya ga cutar shan-inna gwamnati na kokarin yakar sauran cututtukan da suke gallabar yara.
A jawabin fitaccen likitan nan a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Dokta Sani Gwarzo ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki a yaki da cutar shan-inna su kara kaimi kuma a ci gaba da ilimantar da iyaye don ta haka ne za a samu nasarar kawar da cutar.
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma kwararren likita, Dokta Ahmad Abubakar Gumi, ya yi kira ne ga iyaye su rika yarda ana yi wa ’ya’yansu rigakafin cutar shan-inna. Ya ce kwararrun likitoci da kwararru a fannin hada magunguna sun yi bincike a kan allurar kuma sun tabbatar da cewa tana da kyau kuma ba ta da illa ga yara.
Ya jawo hankalin jama’a kan su daina amfani da jita-jita, su saurari bayanai daga kwararrun likitoci da masu ruwa da tsaki a wannan fanni, don yara su tashi da koshin lafiya.
Dokta Gumi ya ce a Saudiyya da sauran kasashen Musulmi ana ba yara rigakafin shan inna don a kawar da su daga kamuwa da cutar.