An shaka wa amarya da ’yan zaman dakinta guba
Wasu samari da ba a san ko su wane ne ba, sun shaka wa wata amarya da ’yan zaman dakinta guba a Unguwa Uku da ke karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, lamarin da ya yi sanaduyyar sumewarta tare da rasuwar daya daga cikin ’yan matan da ke taya takwana daga makwabtanta.Lamarin ya faru ne […]
Wasu samari da ba a san ko su wane ne ba, sun shaka wa wata amarya da ’yan zaman dakinta guba a Unguwa Uku da ke karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, lamarin da ya yi sanaduyyar sumewarta tare da rasuwar daya daga cikin ’yan matan da ke taya ta
kwana daga makwabtanta.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata da daddare lokacin da angon amaryar mai suna Umma ya yi sallama da ita da niyyar tafiya gidan uwargidansa kwana.
Yayar amarya mai suna Atika Yahaya Musa ta bayyana wa Aminiya cewa a ranar Lahadi da misalin karfe goma na dare sun ji ana buga kofa sai daya daga cikin masu taya ta kwana mai suna Hafsa ta je ta bude. Ta ce bude kofar ke da wuya sai samarin su uku suka kutsa kai cikin gidan. Sai Hafsan ta shige ban-daki ta kulle, su kuma samarin sai suka yi kan matar gidan da daya yarinyar da ke taya ta kwana mai suna Nafisa inda suka shaka musu wani abu mai kama da guba. Nan take suka fadi magashiyan suna numfashi da kyar.
Malama Atika ta ce, “Ba mu san abin da ya faru ba, sai washegari Litinin lokacin da yaran gidanmu suka je yawon Sallah gidan Umma inda suka tarar da kofar gidan a kulle, suka bubbuga amma ba a bude ba. Sai suka koma gida suka fadi abin da ke faruwa. Da farko mun dauka gajiyar aikin Sallah ce ta sa ta yin dogon barci, amma da yaran suka koma gidan suka dawo suka ce har yanzu ba a bude kofar ba, ya sa muka yi tunanin ko akwai matsala.”
Ta ce daga nan ne aka shiga buga wayarta amma ba ta daga ba. Hakan ya sa aka nemi mijinta inda ya je gidan ya sa mukulli ya bude kofar. Ana shiga aka
tarar da Nafisa da Umma a kwance, nan da nan aka kwashe su zuwa asibiti, inda aka tabbatar da rasuwar Nafisa aka kuma kwantar da amarya Umma.
Bincike ya nuna cewa samarin da suka aikata wannan aika-aika, ba su dauki ko allura a gidan amaryar ba.
Aminiya ta gano cewa ’yan uwan amarya Umma na zargin hannun Hafsa a cikin wannan lamarin, idan aka dubi yadda Hafsan ta ki sanar da kowa halin da ake ciki tun a daren da lamarin ya faru da kuma kin amsa kiran da aka rika yi ta wayar Umma.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto amarya Umma ba ta samu damar magana ba, sakamakon halin da take ciki na rai kwakwai-mutu-kwakwai, ita kuma marigayiya Nafisa an yi jana’izarta a gidan iyayenta.
Mijin amaryar Malam Hamisu Taura ya yi karin haske cewa a ranar da lamarin ya faru ba ya gida, sai washegarin ranar Litinin da rana sannan ya yi wa amaryarsa waya amma ba ta dauka ba inda ya yi zaton ko ba ta kusa da ne, daga bisani sai aka kira shi aka sanar da shi cewa har yanzu amaryarsa ba ta bude gida ba. Ya ce hakan ya sa ya zo ya bude gidan inda ya tarar da ita da mai taya ta kwana a kwance magashiyyan.
“Ba mu san wadanda suka aikata wannan lamari ba, amma muna addu’ar Allah Ya tona asirin duk wanda ke da hannu a ciki,” inji shi.
Mukaddashin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Mustapha Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce rundunarsu tana gudanar da bincike don gano gaskiyar lamarin.