…An shawarci al’ummar Filato su kaurace wa cin naman bera

Sakamakon cutar zazzabin Lassa da ta addabi wasu jihohin kasar nan ciki har da Filato, Kwamishinan Lafiya na Jihar Mista Kuden Kamshak ya bukaci al’ummar jihar su guji cin naman bera, saboda likitoci suka gano cutar tana yaduwa ne daga beraye.Kwamishinan ya yi kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da ’yan jarida a Jos […]

…An shawarci al’ummar Filato su kaurace wa cin naman bera
…An shawarci al’ummar Filato su kaurace wa cin naman bera

Sakamakon cutar zazzabin Lassa da ta addabi wasu jihohin kasar nan ciki har da Filato, Kwamishinan Lafiya na Jihar Mista Kuden Kamshak ya bukaci al’ummar jihar su guji cin naman bera, saboda likitoci suka gano cutar tana yaduwa ne daga beraye.
Kwamishinan ya yi kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da ’yan jarida a Jos sakamakon barkewar cutar zazzabin Lassa a jihar, inda ya ce an samu bullar cutar Lassa a kananan hukumomi biyar daga cikin 17 na jihar kuma mutum hudu sun mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Kwamishinan ya bukaci jama’a su fahimci lafiya ita ce uwar jiki, don haka ya zama dole su rika kula da lafiyarsu.  Ya ce ya zama dole ma’aikatan lafiya su rika amfani da kayayyakin aikin da suka dace wajen ganin an kawo karshen cutar a jihar da Najeriya baki daya.
“Shawarata ga al’umma ita ce ya kamata su rika tsabtace muhallinsu, sannan su toshe duk ramukan beraye, su tabbatar ba su ci abincin da ya kwana a bude ba, domin beraye za su iya fitsari ko kashi a kai, inda hakan zai zama sanadiyyar yaduwar cutar zazzabin Lassa,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Ina kuma fata ma’aikatan lafiya za su zage damtse wajen ganin su dauki dukkan matakan da suka dace wajen kawo karshen yaduwar cutar zazzabin Lassa.”
Da yake magana game da matakin da gwamnati ta dauka don dakile cutar, Kwamishinan ya ce sun shirya taron horar da ma’aikatan lafiya a kan cutar, sannan gwamnati ta samar musu da kayan da suke bukata wajen yaki da cutar.
“A nan Jihar Filato mun shirya taron kara wa juna sani, mun horar da ma’aikatan lafiya musamman ma daraktoci a bangaren lafiya a matakin farko da jami’an da za su rika wayar da kan jama’a kan cutar, don ganin an kawo karshen cutar,” inji shi.