An shawarci gwamnoni game da ayyukan raya kasa

  Shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga gwamnonin jihohin Najeriya da su rika ci gaba da ayyukan raya kasa da suka gada daga gwamnonin da suka gabata. Sheikh ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da ’yan […]

An shawarci gwamnoni game da ayyukan raya kasa

 

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga gwamnonin jihohin Najeriya da su rika ci gaba da ayyukan raya kasa da suka gada daga gwamnonin da suka gabata.

Sheikh ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos. Ya ce ya kamata duk abin da aka fara ginawa kamar hanyoyin mota ko asibitoci ko makarantu, duk wanda ya zo ya dora a kan wannan aiki da ya tarar. Kada ya yi amfani da siyasa ya dakile wadannan ayyukan raya kasa da wasu shugabannin baya suka fara.

“Duk ayyukan raya kasa da wani gwamna ya zo ya gada, ya dora kan wannan aiki ya kammala domin al’umma su amfana. Ba daidai ba ne gwamnoni su rika watsi da ayyukan raya kasa da suka gada saboda siyasa su ki ci gaba da gudanar da wadannan ayyuka maimakon su kirkiro nasu.”

Malamin ya yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki kan masu tallar magunguna suna yin batsa a kasuwannin kasar nan, domin suna lalata tarbiyar al’umma. Ya ce wannan abu da suke yi ba daidai ba ne a cikin al’ummarmu.

Daga nan ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda gwamnatinsa ta jajirce kan tsaro a kasar nan. Ya ce sakamakon kokarin gwamnatin, yanzu Allah Ya rushe Boko Haram kuma an magance masu kokarin raba kasar nan, ta hanyar fafutukar neman kasar Biyafara.