An shawarci kananan bankuna su karbi kudin Marketmoni don raba wa al’umma
Shugabar karamin Bankin Kasuwanci na Grassroot ta yi kira ga kananan bankunan kasuwanci da ke Jihar Kano da su fito su karbi kudin Marketmoni daga Bankin Masana’antu, don al’ummar jihar su amfana daga kudin, ta bayyana haka a lokacin bikin raba kudin da Bankin ya yi a karo na biyu. Shi dai wannan tallafi na […]

Shugabar karamin Bankin Kasuwanci na Grassroot ta yi kira ga kananan bankunan kasuwanci da ke Jihar Kano da su fito su karbi kudin Marketmoni daga Bankin Masana’antu, don al’ummar jihar su amfana daga kudin, ta bayyana haka a lokacin bikin raba kudin da Bankin ya yi a karo na biyu.
Shi dai wannan tallafi na Marketmoni Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta bullo da shi da niyyar bayar da bashin jari ga kananan ‘yan kasuwa wadanda suka hada da mata da matasa masu sana’a da kuma manoma.
Hajiya Farida ta bayyana cewa har zuwa yanzu bankuna biyu ne kadai ne a JIhar Kano suka karbi kudin wanda kuma ba za su iya gamsar da al’ummar jihar ba duba da irin dimbin yawan al’ummar da Allah ya albarkaci jihar da su.
“Wannan kudi na Marketmoni sama da Naira biliyan 11 suna nan a jibge a Bankin Masana’antu. Kamar yadda aka tsara abin, Bankin Masana’antu zai raba kudin ga jama’a ne ta hanyar hadin kai da kananan bankuna irin namu (Microfinace). Idan har bankunan nan ba su fito sun karbi kudin nan ba akwai yiyuwar mutannen su rasa samun wannan dama ta cin gajiyar shirin, domin har zuwa yanzu da nake magana bankuna biyu ne rak suka karbi wadannan kudade tare kuma da rabawa ga jama’a. Idan mun duba yawan al’aumar Jihar Kano bankuna biyu sun yi kadan su gamsar da su, don haka akwai bukatar sauran bankunan sama da guda 40 su yunkuro su yi kishi su kuma karbi wannan kudade don amfanin al’ummarmu. Idan ba haka ba kuwa sauran jihohin Kudu za su bar mu a baya,” inji ta.
A jawabinta cewa, ta yi lokacin da muka fara mun ba mutum 100, a yanzu kuma za mu ba mutane 133. Muna sa ran nan gaba yawan mutanen zai karu.
“Daga rahotannin da muke samu mutanen da suka karbi wannan kudi a baya sun bunkasa kasuwancinsu da su, kuma suna biyan banki ba tare da matsala ba. Muna bibiyar yadda suke gudanar da al’amuransu idan da matsala mukan yi kokarin magance ta tare da bayar da shawarwari a kan yadda mutum zai bullo wa harkar kasuwancinsa,” inji ta.
Manajan Darktan ta yi kira ga ’yan kasuwa da su rika yin ajiya wacce aka ce maganin wata ana, don idan sun tashi biyan kudin a duk mako su iya biya cikin sauki “baya ga haka kuma akwai bukatar yan kasuwa su karfafa mu’amalolin da suke yi na kasuwancinsu da kuma kungiyoyinsu.”
Har ila yau. ta yi kira ga mata na yankin Arewa gaba daya da su fito su samu lambar Banki ta BbN duba da muhimmancin da lambar ke da ita a gare su. “Idan har matanmu na Arewa ba su fito sun karbi wannan lamba ta BbN ba to suna ji suna gani abubuwan ci gaba zai wuce su. Haka za mu yi ta zama a baya, kasancewar a yanzu idan an kula komai za a yi ana cewa sai mutum yana da lambar banki ta BbN. Ko a yanzu da muke raba wannan kudin na Marketmoni haka muke ta fama da mutane da ba su da wannan lamba. A fito a samu wannan lamba ba ma sai abin neman BbN din ya taso ba, kamar yadda mutum ya san zai karbi katin shaidar dan kasa da na zabe, to haka ita ma wanann lamba take da amfani a zo a karba a ajiye”
Hajiya Fatima Sagir ita ce Shugabar kungiyar ’yan kasuwa mata ta Jihar Kano ta bayyana jin dadinta game da wannan kudi da ’ya’yan kungiyarta ta suka samu inda kuma ta yi kira ga ’yan kasuwa da su fito su yi rajista da kungiya don samun wannan tallafi, kasancewar bankuna ba za su bayar da kudin a daidaikun mutane ba sai a kungiyance. Hajiya Fatima a madadin mata ’yan kasuwa ta sha alwashin matan da suka karbi kudin za su yi amfani da su yadda ya dace tare da mayar da su kamar yadda aka yi yarjejeniya. “Kowa ya san mata da jajircewa akan abin da suka sa gaba, na tabbata mata za su yi amfani da kudin nan yadda ya dace. Mu ba karin aure za mu yi ba, ballantana kudin su tafi a haka. Kowa ya san kudinmu na juyawa ne ba za mu taba yarda su lalace a banza ba. Zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga mata da su fito su yi rajista da kungiyoyin ’yan kasuwa ko na ci gaban al’umma, don wannan kudi mutum ba zai iya samu ba sai ta hanyar kungiya.”
Shi ma wani dan kasuwa mai suna dankaka Saleh da ya samu wannan kudi ya bayyana cewa zai yi amfani da shi yadda ya dace domin zai bunkasa kasuwancinsa da su tare da alkawari mayar da su kamar yadda aka yi alkawari.