An shawarci manoman Yobe su shuka iri mai nuna da wuri
Babban Manajan Hukumar Bunkasa Aikin Gona (ADP) ta Jihar Yobe Alhaji Mustapha Goggobe ya shawarci al’ummar jihar su yi kokarin neman irin shuka da ke nuna cikin hanzari don kauce wa illar fari sakamakon sanarwar da masana ilimin yanayi suka bayar cewa akwai yiwuwar samun karacin ruwan sama a daminar bana. Alhaji Mustapha Goggobe ya […]
Babban Manajan Hukumar Bunkasa Aikin Gona (ADP) ta Jihar Yobe Alhaji Mustapha Goggobe ya shawarci al’ummar jihar su yi kokarin neman irin shuka da ke nuna cikin hanzari don kauce wa illar fari sakamakon sanarwar da masana ilimin yanayi suka bayar cewa akwai yiwuwar samun karacin ruwan sama a daminar bana. Alhaji Mustapha Goggobe ya bayyana haka ne ga Aminiya a Damaturu, inda ya ce, akwai bukatar da manoman jihar su gagauta zuwa hukumar don samun irin shuka ganin wasu sassan jihar sun fara samun ruwan sama. Ya ce tunin hukumar ADP ta kudirin aniyar habaka aikin noma a jihar kasancewar al’ummar mafi yawan al’ummar jihar sun dogara da noma da kiwo ne a harkokinsu na rayuwa. Manajan ya ce daga cikin hobbasar da hukumarsa ta yi shi ne tanadar irin shuka don manoman jihar su amfana ganin cewa a halin yanzu an samun irin shuka mai nuna cikin kankanen lokaci da ya zo daidai da yanayin jihar mai fama da hamada. Ya ce don saukaka wa manoma hukumarsu ta ADP ta tura ma’aikatanta kananan hukumomin jihar 17 don ba manoma shawarwari da jin kokensu game da harkar noma a yankunansu.