An shawarci matasa su hamzarta yin katin zabe da na dan kasa

An shawarci matasa da sauran ‘yan Najeriya da ba su mallaki katin zama dan kasa ko na zabe ba da su hanzarta yi domin amfaninsu a nan gaba. Wata tsohuwar Kansila a karamar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna Hon. Mercy Marcus ne ta bayyana haka ga al’ummarta dake Sabon Garin Kaninkon da ke karamar hukumar […]

An shawarci matasa su hamzarta yin katin zabe da na dan kasa

An shawarci matasa da sauran ‘yan Najeriya da ba su mallaki katin zama dan kasa ko na zabe ba da su hanzarta yi domin amfaninsu a nan gaba. Wata tsohuwar Kansila a karamar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna Hon. Mercy Marcus ne ta bayyana haka ga al’ummarta dake Sabon Garin Kaninkon da ke karamar hukumar Jema’a.

Hon. Mercy ta koka kan yadda ta ga wasu matasa musamman a

gundumarta da ba su damu da yin rajistar ba, duk kuwa da matukar amfanin da katin ke da shi, inda ta bayyana cewa nan gaba komai za ka yi a kasar nan sai ka na da wani shaida karbabbe da zai gamsar da kowace irin hukuma kamar katin shaidar zama dan kasa ko na zabe.

“Don haka wajibi ne ga duk wani mai ruwa da tsaki ya tashi tsaye wajen wayar da kan matasa kan muhimmancin yin katin zama dan kasa. Sannan ina kira ga matasa da su tashi tsaye wajen neman ilmi da kuma abin da za su yi don dogaro da kansu domin bada tasu gudummawar wajen gina kasa da al’ummarta, maimakon jiran ayyuka masu maiko daga wajen gwamnati,” ta bayyana.

Da ta juya kan irin kokarin da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir elRufai ke yi, tsohuwar Kansilar ta jinjina masa kan yadda ya tashi haikan wajen maido da zaman lafiya a jihar Kaduna musamman Kudancin jihar. “Don haka ya zama wajibi mu rungumi juna mu zauna lafiya tare da yafe wa junanmu da kuma manta duk abubuwan da su ka faru a baya don taimakawa kasa ta samu ci gaban da ya kamata.”