An shawarci matasa su tsaya zabe don kawar da tsofaffi

Shugaban Hadaddiyar kungiyar Cigaban Matasa tare da   samar musu ayyukan yi na kasa wato (National Youth Enpowerment Initiatibe Organization) Dakta Shamsuddin Aliyu Maiyasin ne ya furta haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron kungiyar na kasa a Zariya.  Dakta Shamsuddin Maiyasin ya ce matasa su ne kashin […]

An shawarci matasa su tsaya zabe don kawar da tsofaffi

Shugaban Hadaddiyar kungiyar Cigaban Matasa tare da   samar musu ayyukan yi na kasa wato (National Youth Enpowerment Initiatibe Organization) Dakta Shamsuddin Aliyu Maiyasin ne ya furta haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron kungiyar na kasa a Zariya. 

Dakta Shamsuddin Maiyasin ya ce matasa su ne kashin bayan kasar nan, domin sune kashi 65 na mutanan kasar nan, kuma kashi 45 duk sun yi karatun addini ko na zamani, amma sune koma-baya akan   kowane harka na kasa, don haka muka kira taron kunggiyarmu ta kasa domin mu zaburar da matasa da su yi kokarin shiga harkar zabe   a dama da su, kuma wannan kungiyar tana da rassa a kowace jaha a Najeriya, kuma duk kusan kowace jaha ta turo wakili a taron. 

Dakta Shamsuddin ya ci gaba da cewa a yadda ake yi a yanzu idan ka duba zaka ga duk kusan mukamai da ake kai duk tsofaffi ne suke kai ba za ka ga matasa ba, duk da cewa muke da saurin kawo cigaba a kasa.

“Misali idan ka dauko shugaban kasa Yakubu Gawon a lokacin da yayi mulki ya kawo cigaba sosai a kasar nan, kuma a lokacin ko shekara 30 bai cika bay a fara mulkin. Dan haka muke kira ga matasanmu da su fito fili a san da zamansu, kuma fitowar tasu ita ce kawai zai magance mana matsalolin da suke damun mu, kamar rashin aikin yi ga matasa da dai sauransu, kuma ko yanzu taron ya yi nasara domin matasa sun amsa kira,” in ji shi.